Ya kashe matarsa a kan zargin tana neman maza

Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta kame wani mutum mai suna Femi Adebowale bisa zargin kisan matar sa. A sanarwar da kakakin rundunar ya fitar ASP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminya cewa ƙanen marigayiyar ne ya shigar da kara, inda ya shaida cewa wanda ake zargin ya yi ta dukan ‘yar uwarsa, wanda hakan […]

Ya kashe matarsa a kan zargin tana neman maza

Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta kame wani mutum mai suna Femi Adebowale bisa zargin kisan matar sa. A sanarwar da kakakin rundunar ya fitar ASP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminya cewa ƙanen marigayiyar ne ya shigar da kara, inda ya shaida cewa wanda ake zargin ya yi ta dukan ‘yar uwarsa, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta.

Wanda ake zargin Femi Adebowale ya shaida cewa take-taken uwargidan nasa ne musababbin samun rashin jituwarsu, inda ya ce tana yawan  neman maza, har ta kai ga neman maƙwafcinsa da suke zaune a gida guda. Ya ce lokacin da lamarin zai auku ta nemi ya ba ta kudi ta yi shagalin sunan dan da aka Haifa wa ƙanenta, nan take ya ba ta Naira dubu 10, sai ta ce sun yi kadan, shi kuwa dama ganin tana neman maza ne ya sa ya rage yawan kudin da yake ba ta, wanda hakan ne ya yi musababbin rikicin su da ya yi sanadiyar kisanta.

Tuni dai rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta tasa keyarsa zuwa shashen bincike na manyyan laifuka kafin daga bisani a gurfanar da shi a gaban kuliya.