Ya kashe matarsa bayan ta daura niyyar kashe kanta
A makon jiya ne wani mutum a garin Greater Manchester na kasar Birtaniya ya kashe mai dakinsa bisa kuskure yayin da yake kokarin ceto ranta bayan ta daura niyyar yin kunar bakin wake, kamar yadda jaridar Manchester Ebening News ta bayyana. Marigayiyar mai suna, Carol Wolstenholme, ta rasu ne bayan sun fara kokowa da mijin […]
A makon jiya ne wani mutum a garin Greater Manchester na kasar Birtaniya ya kashe mai dakinsa bisa kuskure yayin da yake kokarin ceto ranta bayan ta daura niyyar yin kunar bakin wake, kamar yadda jaridar Manchester Ebening News ta bayyana.
Marigayiyar mai suna, Carol Wolstenholme, ta rasu ne bayan sun fara kokowa da mijin nata mai sauna, Stebe Wolstenholme, bayan da ta fara yi wa kanta rauni a kicin.
Kamar yadda ya bayyana wa kotun da ke sauraron karar, Mista Stebe ya ce: “’Carol ta rasu ne bayan da na yi kokarin kwace wukar da take rike da ita. ”
Ya kara da cewa a lokacin da yake rike da ita ne, sai ya kira lambar neman agajin gaggawa ta 999 domin ya bayyana musu halin da ake ciki. Har ila yau, ya ce lokacin da suke kokowar ya fahimci cewa ba ta lumfashi. Daga nan ne ya ce, “na gaura mata mari don ta farfado, amma ba ta ko motsa ba,” inji shi.
Tun da farko dai an tsare mijin marigayiyar ne bisa zargin kisa, amma daga bisani bayan fahimtar hakikanin abin da ya faru, kotun ba ta iya yanke masa kowane hukunci ba. Kodayake, likitoci sun tabbatar da cewa raunukan da Carol ta yi wa kanta kawai za su iya yin ajalinta.