Ya kashe matarsa bayan ya sassare fuskarta da adda

Wani magidanci dan kimanin shekara 80 da haihuwa a Jihar Akwa Ibom mai suna Daniel Okpo, ana zarginsa da daddatsa matarsa mai suna Alice Ita da adda a fuska, wanda hakan ya yi musabbabin ajalinta. Daniel ya ce ya yi haka ne saboda zarginta da tana kawo maza gidansa. Wannan lamari ya faru a kauyen […]

Ya kashe matarsa bayan ya sassare fuskarta da adda
Ya kashe matarsa bayan ya sassare fuskarta da adda

Wani magidanci dan kimanin shekara 80 da haihuwa a Jihar Akwa Ibom mai suna Daniel Okpo, ana zarginsa da daddatsa matarsa mai suna Alice Ita da adda a fuska, wanda hakan ya yi musabbabin ajalinta.

Daniel ya ce ya yi haka ne saboda zarginta da tana kawo maza gidansa. Wannan lamari ya faru a kauyen Mbiokporo, karamar Hukumar Nsit Ibom.
Da yake yi wa manema labarai karin bayani, Mataimakin Kwamishinan ’Yan sandan jihar mai kula da sashen aikata miyagun laifuka ACP Mike Okoli ya ce: “Wanda ake zargin ya lababo, matarsa tana barci ya dinga sarar ta da adda a fuska har sai d a yaga rai ya yi halinsa tukuna ya hakura.” Koda aka sanar wa da rundunarsu aka kama mai laifi, bai musunta ba, ya amsa laifinsa cewa shi ya aikata hakan.
Aminiya ta ji ta bakin mai laifin da ake zargi, kan ko me ya yi zafi tsakaninsa da matarsa; ganin cewa shi ba yaro ba ne bare a ce kuruciya ce, ga shi kuma ya kai jallin manyanta? Sai ya ce: “Raina ne ya baci saboda na lura matata tana kwartanci, tana kawo maza gidana; shi ya sa na dauki doka a hannuna amma dai na yi nadamar abin da na aikata.”
Mataimakin Kwamishina ya ce ba tare da bata wani lokaci ba za su mika shi gaban kotu, domin ta ci gaba da nata aikin.