Ya kashe matarsa don ta zarge shi da neman matan makwabta
‘Yan sanda a Jihar Oyo, sun kama wani mutumi mai suna Nojeem Adeyemo, bisa zargin kashe matarsa mai suna Rukayat, ta hanyar saranta da adda inda ya guntile hannun damanta a dalilin yawan zarginsa da neman matan makwabta. Al’amarin ya auku ne a ranar lahadi 31 ga watan jiya a cikin gidan wannan mutumi da […]
‘Yan sanda a Jihar Oyo, sun kama wani mutumi mai suna Nojeem Adeyemo, bisa zargin kashe matarsa mai suna Rukayat, ta hanyar saranta da adda inda ya guntile hannun damanta a dalilin yawan zarginsa da neman matan makwabta. Al’amarin ya auku ne a ranar lahadi 31 ga watan jiya a cikin gidan wannan mutumi da ke unguwar Orita, a garin Saki.
Nojeem Adeyemo, mai shekaru 31 da haihuwa manomi ne, ya yi kokarin tserewa daga gidan nasu bayan takaddama tsakaninsa da matar tasa da ya guntile wa hannu amma makwabta suka cafke shi suka mika shi shi ga ’yan sanda tare da garzayawa da matar zuwa asibiti, inda ta rasu saboda yawan jinin da ta rasa.
Bayan kama mutumi a garin Saki, ‘yan sanda sun mika al’amarin ga sashen binciken manyan laifuka na ‘yan sandan farin kaya (SCID) da ke karkashin jagorancin ACP Dasuki Galadanci, a Iyaganku Ibadan domin ci gaba da bincike.
Mutumin da ake tsare da shi a kan zargin kashe matarsa ya shaidawa wakilinmu cewa, “mata ta Rukayat, mutuniyar kirki ce, ita ce take kai kawo da daukar dawainiya ta a duk lokacin da na samu lalurar rashin lafiya. Har ma mun kammala aikin sabon gidan da muka gina tare. Sai dai, tana yawan zargin ina neman matan makwabta wanda na sha karyata zargin nata tare da gargadin ta daina yin hulda da miyagun kawaye da suke yi mata ingiza mai kantu ruwa. A karshe dubi irin halin da tasa shaidan ya jefa ni a ciki yanzu.”
“A ranar da wannan al’amari ya auku, ina dawo wa daga gona da misalin karfe 10 na safe sai Rukayat, ta fara cin mutunci na zargin aike wa da mutane cikin mafarkinta da za su hallaka ta. Ta yi kururuwar cewa, tana yawan ganin wasu dodanni da suke biye da ita a cikin mafarkinta, har ma daya daga cikin irin matan da take gani a cikin mafarki ta bayyana a fili tana cin mutuncinta a wannan rana kafin mu kai ga takaddamar ta mu,” inji Nojeem Adeyemo, wanda ya ci gaba da cewa, “a daidai wannan lokaci ne hayaniya ta kara ruruwa har tayi wuf ta kwace addar da ke hannuna tana cewa, bari ta kashe ni kafin in kashe ta, amma na ci karfinta na kwato addar daga hannunta na kai mata sara, wanda ya guntile hannun daman ta. A gaskiya na yi nadamar aikata hakan.”Inji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Oyo, Uwargida Olabisi Okuwobi-Ilobanafor, ta tabbatar da aukuwar wannan al’amari, inda ta ce da zarar an kammala bincike za a mika wanda ake zargin kotu, domin yanke masa hukumci.