Ya kashe matarsa kan zargin kwartanci

Ma’auratan sun kulle kansu a cikin gida suna fada dauke da makami kan zargin matar da cin amanar aure.

Ya kashe matarsa kan zargin kwartanci

Wuka

Ana zargin wani magidanci da caka wa matarsa wuka ya kashe ta kan zargin cin amanar aure.

’Yan sanda sun tabbatar cewa magidancin mai shekaru 34 ya yi wannan aika-aika ne a garin Ado-Ekiti, hedikwatar Jihar Ekiti.

Kakakin ’yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya ce ’ya’yan ma’auratan ne suka kawo rahoton faruwar lamarin.

Shaidu a layin Christ Avenue inda abin ya faru sun bayyana cewa kowanne daga cikin ma’auratan yi yi amfani da makami a lokacin da suke rikicin.

Wani shaida da ya ne,i a boye sunansa ya ce sai da ma’auratan suka aiki babban dansu sannan suka kulle kansu a cikin gida suka fara gardama kan zargin cin amanar auren, inda suka yi wa juna raunuka da makami.

Wani shaids ya ce mutumin jami’in tsaro ne, matar mai shekaru 32 kuma tana aiki ne a wani kantin sayar da magunguna

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa

Gwamnati ta ba da hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara

NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Suke Haddasa Turmutsutsu A Najeriya