Ya kashe matarsa ya jefar a gefen kududdufi

Wani magidanci mai shekara 40 mai suna Tukur da ke kauyen Sha’iskawa kusa da Yadakwari a karamar Hukumar Garun Malam a Jihar Kano, ya shiga hannun ’yan sanda bisa zargin kashe matarsa Lawanzana, mai shekara 30 cikin dare ranar Lahadi inda ya jefar da gawarta a gefen kududdufi.Wani mazaunin kauyen da aka sakaya sunansa, ya […]

Ya kashe matarsa ya jefar a gefen kududdufi
Ya kashe matarsa ya jefar a gefen kududdufi

Wani magidanci mai shekara 40 mai suna Tukur da ke kauyen Sha’iskawa kusa da Yadakwari a karamar Hukumar Garun Malam a Jihar Kano, ya shiga hannun ’yan sanda bisa zargin kashe matarsa Lawanzana, mai shekara 30 cikin dare ranar Lahadi inda ya jefar da gawarta a gefen kududdufi.
Wani mazaunin kauyen da aka sakaya sunansa, ya ce “Mun wayi gari ne kawai muka ga gawar matar a yashe a gefen rami, kuma mijin bai gudu ba har ’yan sanda suka zo suka kama shi.”
Mai Unguwar Sha’iskawa, Malam Na’Allah Daudu ya shaida wa Aminiya cewa “Da misalin karfe 6:00 na safiyar Litinin ne, shugabana maigarin Yadakwari ya kira ni ya shaida min abin da ya faru, muka je inda gawar take.” Y a ce a lokacin da mutane suka taru ana kallon gawar har da mijinta, daga nan suka nuna shi ga ’yan sandan Kadawa suka kama shi. Ya ce ’yan sandan sun ga jini a rigarsa duk da ya sa wuka ya yanke wurin da jinin ya taba. Daga nan ne suka shiga da shi gidansa ya nuna karfen karanshof da ake zargin ya buga mata a kai ta rasu.
Ana zargin Tukur wanda ya fio daga kauyen Wailari a ankin Makoda da ke jihar da shaye- shaye da ayyukan tsubbu, yayin da matarsa ta fito daga Anchau a Jihar Kaduna.
An ce suna da ’ya’ya biyu, kuma mijin ya fara zama a Yadakwari ne misalin shekara daya, kafin ya koma Sha’iskawa wata shida da suka gabata.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Kano, Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce “Mutumin ya ce ya yi haka ne bisa zargin ta da kula maza a waje. Yanzu haka na tsare a sashin binciken manyan laifuffuka, kuma bayan bincike za a gurfanar da shi a gaban kotu.”