Ya kashe mayakan ISIS bakwai don daukar fansar dansa a Iraki
Wani mutumin kasar Iraki mai suna Basil Ramadan da mayakan ISIS suka kashe masa da mai suna Ahmed Basil ya kashe mayakan kungiyar ISIS a wani mataki na daukar fansa. Mayakan ISIS sun kashe Ahmed Basil ne tare da wasu mutane ta hanyar bindige su kamar yadda wata jaridar Iraki ta ruwaito.Basil Ramadan, wanda aka […]
Wani mutumin kasar Iraki mai suna Basil Ramadan da mayakan ISIS suka kashe masa da mai suna Ahmed Basil ya kashe mayakan kungiyar ISIS a wani mataki na daukar fansa.
Mayakan ISIS sun kashe Ahmed Basil ne tare da wasu mutane ta hanyar bindige su kamar yadda wata jaridar Iraki ta ruwaito.
Basil Ramadan, wanda aka ce ya kai shekara 60, ya yi amfani da bindiga kirar AK-47 ne wajen harbe mayakan na ISIS a wani wurin duba abubuwan hawa a garin Tikriti wani birni da ke Arewa maso Yamma da birnin Baghdad da ke karkashin ISIS, kafin shi ma a harbe shi.
Ahmed Basil mai shekara 18, yana daga cikin mutum takwas da ISIS suka zartar wa hukuncin kisa a Janairun bana, bisa zargin suna yi wa gwamnatin kasar leken asiri a cikin kungiyar. ISIS ta fitar da wani hoton faifan bidiyon zartar da hukunci kan Basil da sauran mutum bakwai, wadanda aka ce dukkansu ’yan sanda ne da ake zargi da tona wa gwamnati aikace-aikacen ISIS.
Hotunan da aka yi musu take da ‘Ranar Hisabi,’ sun nuna mutanen bakwai sanye da jajayen kaya irin na fursunonin Guantanamo Bay da Amurka ta tsare mayakan Taliban.
An bayyana sunayen wadanda aka zartar wa hukuncin ciki har da Ahmed, kuma a cikin bidiyon an zarge shi da bayar da bayanan inda gidajen mayakan ISIS suke.
Jagoran mutanen mai suna Kyaftin Hossam Salah Bnosh a cewar ISIS sun shiga kungiyar ta ISIS ce, kuma bayan sun shiga cikin jami’an tsaronta sai suka shiga bayar da bayanai ga gwamnatin Iraki cikin sirri, inda aka zarge su da ba gwamnatin Iraki rahotannin sirri don gano inda za ta kai hari ta jiragen sama kan mayakan ISIS.
An kama daya daga cikinsu mai suna Marwan Habib Sa’id yana bayar da bayanai ga gwamnatin Iraki, bayan ya shiga cikin jami’an tsaro na ISIS. Kuma hotunan sun nuna an rufe idanuwan fursunonin tare da daure hannuwansu ta baya, aka sa suka yi tsallen kwado zuwa bakin kogin da ake zargin na Tikiriti ne, inda wasu mayakan ISIS suka harbi kowane dayansu da harsashi dai-daya a kai.