Ta kashe mijinta saboda ya ki sayarwa dansu kayan Kirisimeti
Wata malamar makaranta mai zaman kanta a Legas ta hallaka mijinta har lahira bayan da takaddama ta kaure a tsakanin su a kan riga da takalmin Kirisimeti da dansu zai sanya a ranar. Wacce ake zargin mai suna Jacinta Igboke, ta hassala ne bayan da mahaifin yaron wanda basu kai ga yin aure ba ya […]
Wata malamar makaranta mai zaman kanta a Legas ta hallaka mijinta har lahira bayan da takaddama ta kaure a tsakanin su a kan riga da takalmin Kirisimeti da dansu zai sanya a ranar.
Wacce ake zargin mai suna Jacinta Igboke, ta hassala ne bayan da mahaifin yaron wanda basu kai ga yin aure ba ya yi burus ya ki ya sai masa kayan Kirisimeti, inda ita ta kudira ta sai masa riga ta ce shi ya sayi takalmi, amma ya yi halin ko in kula, inda ta shaida cewa taje ta same shi a rumfarsa da ke kasuwa a yankin Ojo a Legas, inda ta bukaci ya bada kudin takalmi sai ya ki ya hankadeta ita kuma a kokarinta na kare kanta sai ta daba masa wuka, ta ce bata zaci zai mutu ba, kana tayi ta kaicin yadda ya ki bai wa dansu kulawa inda ya maida hankali yana kokarin yin auren wata matar ta daban.
A baya iyayen marigayin sun dau matakin hana shi auren ta ne inda suke kokarin aura masa wata matar ta daban a watan Janairun shekarar 2020.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wace ake zargin tana hannun rundunar inda ake ci gaba da bincikenta kafin a kai ga gurfanar da ita a kotu.