Ya kashe mutum saboda giyar Naira 200

Wani matashi dan kimanin shekara 23 mai suna Taiwo Olatokunbo ya shiga tsaka-mai- wuya bayan da gardama ta kaure a tsakaninsa da wani mutum da suka hadu a gidan sayar da giya, lamarin da ya sanya shi kashe mutumin mai kimanin shekara 32 a kan giyar Naira dari biyu. Mai magana da yawun Hukumar ’Yan […]

Ya kashe mutum saboda giyar Naira 200

Taiwo Olatokunbo da ake zargin kashe mutum a kan giyar Naira 200

Wani matashi dan kimanin shekara 23 mai suna Taiwo Olatokunbo ya shiga tsaka-mai- wuya bayan da gardama ta kaure a tsakaninsa da wani mutum da suka hadu a gidan sayar da giya, lamarin da ya sanya shi kashe mutumin mai kimanin shekara 32 a kan giyar Naira dari biyu.

Mai magana da yawun Hukumar ’Yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne a yankin Ijagun a Ijebu-Ode da ke jihar. Ya ce matar da ke sayar da giyar ce ta sanar da su ’yan sandan game da lamarin.

“Matar mai suna Temitope Adedayo ta shaida mana cewa wanda ake zargin, Taiwo Olatokunbo ya shiga rumfar da take sayar da giya da misalin karfe 3 na ranar Asabar din da ta gabata, inda ya sayi giya samfurin ‘More’ wacce kudinta ya kama Naira 200. Bayan ya shanye kwalba guda sai ya ki biyan kudin. Hakan ne ya sanya daya daga cikin abokan cinikinta mai suna Christian sanya baki a lamarin, inda ya nemi Olatokunbo ya biya kudin giyar Naira 200; lamarin da ya sanya gardama ta kaure a tsakaninsu nan take. Olatokunbo ya fasa kwalbar giyar, ya daba wa Christian, inda aka garzaya da shi babban asibitin jihar da ke Ijebu-Ode, inda a can ya mutu a daidai lokacin da ake kokarin ceton rayuwarsa,” inji shi.

Kakakin ’yan sandan ya kara da cewa Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Ahmad Iliyasu ya ba da umarnin tura wanda ake zargin zuwa sashin bincikan miyagun laifuffuka na hukumar domin zurfafa bincike.