Ya kashe Naira miliyan 200 don zanen tattoo a jikinsa

A shekarun da suka gabata, Remy ya yi tattoo a kusan kowane inci na jikinsa.

Ya kashe Naira miliyan 200 don zanen tattoo a jikinsa

Wani mai suna Remy, dan kasar Kanada, ya ce ya kashe fiye da Naira miliyan 200 wajen yi masa zanen tattoo a jikinsa kuma ya ce babu abin da zai hana shi son zanen.

Remy ya yi rubutu game tattoo a shafin sada zumunta na Instagram inda ya samu magoya bayansa da suka kai 77,100.

Mutumin da ke da dubban zanen tattoo ya shafe shekaru da yawa yana zama a kujerar da ake yi masa zanen inda sama da kashi 96 cikin 100 na jikinsa aka rufe take da zanen tattoo.

Tsohon mai sana’ar dafa abinci ya sha wallafa sabon salon zanensa a a shafukan Instagram inda yake alfahari da ɗimbin magoya baya 77,100 da ke sha’awar kallonsa kullum.

Ya maimaita wasu wuraren a jikinsa sama da sau 30 kuma da alama bai tsaya nan ba.

Yanzu a cikin wani sabon sakon da ya wallafa a baya-bayan nan a kafofin sada zumunta na zamani, mai son gyaran jikin ya bayyana adadin kuɗin da zanen tattoo a jikinsa a ya lakume.

A cikin wani faifan bidiyo, Remy ya amsa tambayar wani masoyinsa wanda ya yi tambaya game da farashin zanen jikinsa.

Ya ce: “Ina gaya wa mutane na kashe kusan Fam dubu 115, (kwatankwacin Naira miliyan 219 da dubu 922 da 895) a kusan shekara guda ko fin haka.

“Amma ba lallai ba ne, ni ma ina bin diddigi, ina jin daɗi yayin da nake tafiya ina burge mabiyana.

“Kamar idan na fita cin abinci ko zuwa kallon fim da abokai a lokacin ina burge su suna jin daɗi, fiye da yadda kuke tunani,” in ji shi.

A shekarun da suka gabata, Remy ya yi tattoo a kusan kowane inci na jikinsa. Hannu, cinyoyi, baya har da duwawunsa duk an yi musu ado da zane-zane masu launi iri-iri. Kawai ya bar wani ƙaramin ɓangaren fuskarsa da bai taɓa ba ne.

Kuma Remy yana son huda fatarsa, tare da sa ’yan kunne a fuskarsa.

Tun lokacin ya yaɗa hotunansa jikinsa shafin sada zumunta, yawancin magoya baya suka shiga shafin suna sharhi.

Wani ya ce: “Ina gaya wa mutane irin wannan abu lokacin da suka ce na batar da kuɗi a kan zanen tattoo, cewa a mashaya ko zaurunka nishadantarwa da sauransu. Ina yin tattoo, shi ne abin da nake yi don jin dadi.

“Kuma a zahiri wani abu ne da zan iya tafiya da shi kabari.”

Wani ya rubuta masa cewa: “Kai mutum ne mai kwalliya gaba ɗaya! Siffarka na haɓaka! Don ta musamman ce kuma daban. Muna son ka duka.”

Wani kuma ya ce: “Ina son zanen kwalliyar.”
Sai na ƙarshe ya ce: “Ka kula da kanka.”

Remy ya ce kusan kashi 100 na jikinsa an rufe shi da zanen tattoo. Daga sama har kasa, kuma an yi ittifakin ya shafe sama da sa’o’i 2,200 ana yi masa zanen a fata.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda