Ya kashe surukinsa kan kai matarsa asibiti
A makon da ya gabata ne mutanen unguwar Tsohon kafi da ke cikin garin Kazaure a jahar Jigawa suka wayi gari ranar Juma’a da wani lamari mai firgitarwa da ya tayar da hankalin mazauna yankin inda aka kashe wani matashi mai sana’ar awo da ake kira Alhaji Sa’adu da wadansu mutane da ba a san […]

A makon da ya gabata ne mutanen unguwar Tsohon kafi da ke cikin garin Kazaure a jahar Jigawa suka wayi gari ranar Juma’a da wani lamari mai firgitarwa da ya tayar da hankalin mazauna yankin inda aka kashe wani matashi mai sana’ar awo da ake kira Alhaji Sa’adu da wadansu mutane da ba a san ko su wanene ba suka aikata.
Makasan sun je gidansa ne da misalin karfe 11 da kwata na dare ranar Alhamis dauke da muggan makamai, suka tsaya a kan katangar kofar gidansa wani ya shiga gidan suka kama shi da karfin tsiya suka yi amfani da bindiga suka harbe shi a makogwaro ya fadi a mace.
Marigayi Alhaji Sa’adu mutum ne da ya yi fice wajan taimaka wa mata masu sana’ar hannu, musamman matan karkakara da suke yin sana’ar kulikuli da tuyar kosai, kasancewar yana sayar da wake ne da gyada da sauran kayan amfanin gona.
Wadanda suka san shi sun bayar da shaidar cewa shi mutum ne da ba ya son tashin hankali a tsakaninsa da jama’a, lamarin da ya haifar da zarge-zarge da mutane da ke unguwarsu suke yi game da kisan nasa.
Wakilimmu ya samu damar tattaunawa da iyalan marigayin, inda ya fara da mahaifiyar marigayin Hajiya Altine, wadda aka fi sani da Tine. Ta ce lamarin ya yi matukar tayar musu da hankali, domin a iyakar saninta tun daga kuriciyarsa har zuwa lokacin da ya koma ga mahaliccinsa ba a taba kawo kararsa gida, ta ce ta yi mamakin matakin da mutanen suka dauka na raba ta da danta, kuma gashi ba su dauki ko sisi ba a cikin dukiyarsa.
Duk da haka ta ce ita ba ta zargin kowa, domin ba ta ji komai daga kowa ba da zai sa ta zargi wani a kan lamarin. Don haka ta roki jama’a su taimaka musu da addu’a Allah Ya tona asirin duk wadanda suke da hannu wajen yi wa danta kisan gillar. Ta kuma bukaci jami’an tsaro su dauki matakan bincike a kan kisan da aka yi wa danta.
Hajiya Altine kuma ta roki masu hannu da shuni su taimaka musu, kasancewar dan nata ya rasu ya barta da kananan yara, gaba dayansu babu wanda ya kai shekara goma a cikinsu.
Ita kuwa matar marigayin Hajiya Aisha Ya’u cewa ta yi, suna kwance a daki ita da mijinta da misalin karfe goma sha daya da minti goma sha biyar na dare ranar Alhamis, sai ta ji ana bugun kyauren kofar gida, sai mijin ya fita domin ko ya ga waye, fitarsa ke da wuya sai ta bi shi saboda a lokacin an dawo da wuta tana karasa kallon wani kaset, tana fita sai ta ga mutum a kan katangar kofar gidansu a tsaye yana dauke da makami, ganin haka sai ta yi kururuwa tana neman agaji, da ta ga sun kama mijinta da kokawa sun fita da shi kofar gida sai ta yi cikin gida ta shaida wa mahaifinsa, lamarin da ya sa mazan gidan, ciki har da mahaifinsa Malam Ibrahim suka fito domin kawo masa dauki, kafin su karaso, matar ce ta fara dawowa wajen mijin, tana zuwa sai taji ya yi kara, ashe a lokacin sun harbe shi ne a makogoro, tana zuwa sai ta ganshi kwance a cikin jinni. Sai ta ce wa wani karamin kaninsa Mu’azu ya hanzarta kai shi asibiti, sai ya ce mata “ba kya gani ga makogaronsa a waje, ai ya mutu.’’ Daga nan ne ta san mijinta ya mutu. Aisha ta ce, mutanen su uku ne, kuma babu wanda ya dauki komai a gidan, wani kwararo siriri suka bi suka yi yamma, daga nan suka karkata suka yi Arewa suka gudu, ba a kama kowa a cikinsu ba saboda suna da bindiga babu wanda ya tunkare su.
Ta ce a gaskiya ita kam ba ta zargin kowa, domin tasan mijinta yana zaune lafiya da abokan sana’arsa kuma ba shi da abokin fada.
Ta ce a yanzu haka mutanen unguwar ba su yin barci saboda barayi sun addabe su, don haka ta roki gwamna Lamido na jahar Jigawa ya kawo musu dauki.
Ta bayyana cewa suna zaune lafiya tare da mijinta, domin shi mutum ne da ba ya rike al’amari a ransa kuma abin duniya bai rufe masa ido ba, sannan baya kyashin kyautata wa ‘yan uwansa da kuma mutanen unguwa, mutum ne mai tsantseni.
Shi kuma mahaifin marigayin, wato Malam Ibrahim cewa ya yi, marigayi Sa’idu ya rasu ya bar matarsa Aisha da yara hudu da mahaifiyarsa tare da shi kansa, yana da shekara 35.
Ya ce kisan da aka yi ya sa jama’a na tunanin ko matsafa ne, wadansu kuma na ganin ko wadansu ne suke jin haushinsa.
Mahaifin marigayin ya ci gaba da cewa, suna nan suna gaya wa Allah domin duk wadanda suke da hannu wajen yi wa dansa kisan gilla sun bayyan kansu da kansu, saboda a baya an taba irin haka kuma Allah Ya tona asirin wadanda suka yi kuma an hukunta su.
Wakillimmu ya jiwo a wata majiya cewa ‘yansanda sun kame wani mutun da ake zargin yana da alaka da kisan saboda ya taba yin ikirarin cewa sai ya halaka shi kuma wai har an samu makamai a gidan wanda ake zargin
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ASP Audu ya tabbatar da faruwar labarin, ya ce hakika an yi kisan kuma ‘yansanda sun yi kame a wata Unguwa, sai dai wadanda suka yi kamen ‘yan Operation Salama ne.
Da yake karin haske dangane da lamarin, Sakataren Mai martaba sarkin Kazaure, Alhaji Muhammed Nuhu, ya ce masarautar Kazaure ba ta da labarin cewa mutumin da ake zargin shi ne ya aikata kisan, ko yana da alaka da Boko Haram, kuma ya musanta batun da ake yi cewa wai antaba gurfanar da shi a fadar, ya ce ko kusa fada ba ta da wani cikakken bayani a kan wanda ake zargin ba.
Shi ma shugaban ‘yansanda na yanki, Mista Offfion (DPO) ya ce ya tattara duk bayanai ya tura wa hedikwatar ‘yansanda ta jahar da ke Dutse.
Shi kuwa mahaifin yaron da ake zargin dan Boko Haram ne da kuma ake zargin shi ne ya yi wa marigayi Sa’adu kisan gilla, mai suna Malam Suleiman Ibrahim cewa ya yi babu abin da zai ce, domin a iyakar saninsa bai san dansa yana harkar Boko Haram ba, shi dai ya san dansa yana harkar saye da sayarwa da yin markaden kayan miya, daga baya aka ce ya daina ya koma sayar da kankana. Ya ce lamarin ya ba shi tsoro, saboda shi ne ya nema wa dansa auren kanwar wanda aka ce shi ne ya halaka shi.
Ya ce kafin a kama dan nasa sai da ya je ya yi wa mahaifin Alhaji Sa’adu ta’aziyyar rashin dansa, domin akwai zuminci da abokantaka a tsakaninsu.
Cigaba a shafi na 3
Daga shafi na 2
Ya kara da cewa, kafin ‘yansanda su kama dan nasa mai suna Ibrahim Alkairi, ya fi wata biyar ba ya zuwa gidansa, don haka ba shi da wani labari a kan dan nasa ballantana ya san halin da yake ciki, kasancewar Ibrahim magidanci ne ba yaro ba.
Ita ma mahaifiyarsa Hajiya Ramatu cewa ta yi Ibrahim Alkairi mutum ne mai kwazo da kokarin neman abin kansa, saboda aiherinsa ne mutane suke masa lakabi da alkairi, domin ba ya tsada a wajen sayar da kayan miya, gashi da sauki a wajan sana’arsa ta markade
Ta kara da cewa da ta samu labarin kama danta da laifin kisan wan surukarta ba ta ji dadi ba, domin ya watsa musu zuminci, in dai har shi ne ya aikata kisan. Ta nemi hukuma ta aiwatar da bincike mai zurfi a kan lamarin, idan shine yana da hannu a yi masa hukuncin da ya dace.
Ita kuwa kanwarsa Hajiya Maryam Ibrahim cewa ta yi an jima ana baza jita-jita a kan cewa wanta yana da alaka da Boko Haram, amma babu wata cikakkiyar shaida da za ta tabbatar da hakan, domin ba a taba ganinsa da wani dan kungiyar ba, bai kuma taba barin garin Kazaure ba daidai da kwana uku, amma mutane suna ta baza jita-jitar cewa wai yana zuwa Borno da Yobe wajan ‘yan Boko Haram yana kullle-kulle.
Ta ce lamarin yana da rikitarwa, mai warware shi sai dai Allah, domin yayanta ba ya shiga lamarin jama’a, me yiwuwa yana da abokan adawa ne wadanda take tunanin ba sa kaunarsa shi ya sa suke yi masa bita-da-kulli.
Ita kuwa matar wanda ake zargin, wato kanwar shi marigayin mai suna Aisha Ibrahim cewa ta yi ita ba za ta sake yin aure da tsohon mijin nata ba, ita da komawa gidansa har abada, domin shi mutum ne da baya barin matarsa ta sada zuminci da ‘yan uwanta, ba ya barin zuwa unguwa ko ta kama, ba ya barin matarsa ta je asibiti, ya raba ta gaba daya da ‘yan uwanta.
Game da zargin da ake yimasa na alaka da Boko Haram kuwa, cewa ta yi babu wata shaida a kan zargin da ake wa mijinta, domin ita ba ta taba ganinsa da ko da wuka ba ballantana bindiga ko wani sinadarin hada bama-bamai a gidansa. Ta ce idan ma yana yin wannan harka ita ba ta taba sani ba tsawon zamanta da shi, kuma akalla sun kai sama da shekara bakwai suna tare, ba ta taba ganinsa da wani makami ba sai dai wukar da yake yanka kayan miya ko kankana.
Dangane da zargin cewa wai mijinta ya ce zai kashe yayanta kuwa, ta ce a gabansa yayanta ya je ya dauko ta daga gidan mijin nata suka je asibiti, iyakar abin da ta san mijinta ya ce wa yayanta shi ne, idan ya kai ta asibiti ya sake ta, haka kuwa aka yi, ya dauke ta zuwa asibiti daga nan ya sake ta, lamarin da ya sa take zaune a gida, amma ta ce ba ta ji lokacin da ya ce wai zai kashe yayanta ba, “wannan dai maganganu ne na mutane kuma Allah kadai Ya san gaskiya.” Inji ta.
Ta kara da cewa a iyakacin saninta mijinta ba shi da alaka da Boko Haram kuma ba shi da wani abokin fada a duk fadin Kazaure. Kuma da ake cewa wai yana yawaita tafiye-tafiye zuwa Borno da Yobe ta ce karya ne, mijinta tun da ya aure ta ba ya zuwa ko dambatta ya kwana, kullum yana Kazaure har suka rabu.
Wani wanda yake kusa da gidansa ya bada shaidar cewa gidan wanda ake tuhumar tun da ya rabu da matarsa Aisha ba ya bude shi, kullum a kulle yake, kuma suna jin maganganun mutane maza da mata a gidan, kuma kullum ana ganinsa da manya manyan biredi uku yana tsallakawa ta kan katanga, ba ya bude kofa, amma daga lokacin da aka yi wannan kisan sai suka daina jin motsin kowa a gidan.
Ya ce kafin faruwar lamarin wanda ake zargin sun taba rigimi da wani yaro mai babur din haya har ya yi ikirarin zai halaka shi kuma wai ya taba furta cewa zai kashe Alhaji Sa’adu saboda ya yi sanadin rabuwarsa da matarsa, wanda ya sanya aka ankarar da jami’an tsaro suka je gidan, lamarin da wadansu suka ce kafin a kama shi sai da jami’an tsaro sukayi musayar wuta da suka fi karfinsa suka kama shi.
Kakakin rundunar hadin gwiwa ta JTF da ke Kano, Kaftin Ikedichi Iweha ya ce bayan jami’ansu sun yi bata-kashi sun kama wanda ake zargin da sanyin safiyar ranar Lahadi da ta gabata, kuma an kubutar da mata uku da kananan yara uku a yayin samamen.
Ya ci gaba cewa, a binciken farko da suka yi sun fahimci cewa wanda ake zargin yana hada bama-bamai ne kuma a gidansa ne ake tsarin ta’addancin da ake yi a Kano.
Ya ce an samu bindigogi kirar AK 47 guda biyar a gidan da jigidar harsashi guda biyar da harsashi na musamman guda 333 da abubuwa masu fashewa iri-iri.