Ya kashe tsohuwar matarsa kuma ya kashe kansa

A makon jiya ne al’ummar Unguwar Zango Kwajalawa a karmar Hukumar Ungogo a Jihar Kano suka tashi da alhinin wani mugun al’amari inda wani mazaunin unguwar mai suna Hambali Muhammad ya kashe tsohuwar matarsa sannan ya kashe kansa a daidai lokacin da yake kokarin bikon matar. Majiyarmu ta ce Hambali Muhammad ya dauki wannan mataki […]

Ya kashe tsohuwar matarsa kuma ya kashe kansa
Ya kashe tsohuwar matarsa kuma ya kashe kansa

A makon jiya ne al’ummar Unguwar Zango Kwajalawa a karmar Hukumar Ungogo a Jihar Kano suka tashi da alhinin wani mugun al’amari inda wani mazaunin unguwar mai suna Hambali Muhammad ya kashe tsohuwar matarsa sannan ya kashe kansa a daidai lokacin da yake kokarin bikon matar.

Majiyarmu ta ce Hambali Muhammad ya dauki wannan mataki ne saboda kin amincewa da tsohuwar matarsa mai suna Hajara Maisoda ta yi a kan su mayar da aurensu.
Shaidu sun ce marigayi Hambali ya yi amfani da wuka ne wajen kashe tsohuwar matarsa inda ya daddaba mata wuka a wuya da cikinta, kafin ya daba wa kansa wukar a ciki har sai da kayan cikinsa suka fito waje inda daga baisani ya ce ga garinku nan.
Malam Muhammad Sani Kwajalawa makwabcin su Hajara ya ce ’yar marigayiya Hajara ce ta fito tana ihu cewa mahaifinsu ya kashe mahaifiyarsu kuma ya kashe kansa. “diyar marigayiyar ta shaida mana cewa mahaifinsu ya kashe mahaifiyarsu a kan suna
jayayya kan da komen da yake so ta yi gidansa, inda ita kuma ta ki amincewa. Muna jin haka sai muka nufi gidan, muna shiga zaunren gidan muka iske gawarwakin mijin da matar a yashe cikin jini. Mun iske matar ta cika, sai dai shi duk da kayan cikinsa na waje yana da sauran numfashi. Sai aka dauke shi zuwa asibiti inda daidai lokacin Sallar Asuba ya ce ga garinku nan,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce jami’ansu sun halarci wurin da al’amarin ya faru, abin da kawai ya rage musu shi ne tattara bayanai game da marigayin da sauransu.