Ya kashe ubangidansa don ya turmushe dukiyarsa

A ranar litinin da ta gabata ne wani matashi dan shekara 28, mai suna Bello Ubandawaki, ya yi wa ubangidansa da ake kira Alhaji Yahaya Sa’idu Andare, wanda shi ne direktan kudi a ma’aikatar kula da kananan hukumomi ta jihar Kebbi yakan rago a Kwannawa kusa da Sakkwato, da ake zargin ya yi haka ne […]

Ya kashe ubangidansa don ya turmushe dukiyarsa

Bello, wanda ake zargi da yanka ubangidansaMarigayi Alhaji Yahaya Sani Jabbo, aminin marigayi Alhaji YahayaA ranar litinin da ta gabata ne wani matashi dan shekara 28, mai suna Bello Ubandawaki, ya yi wa ubangidansa da ake kira Alhaji Yahaya Sa’idu Andare, wanda shi ne direktan kudi a ma’aikatar kula da kananan hukumomi ta jihar Kebbi yakan rago a Kwannawa kusa da Sakkwato, da ake zargin ya yi haka ne domin ya durmushe dukiyarsa da suka hada da filaye da gidaje da shi kadai ne ya san inda suke.
 Wani babban aminin marigayin mai suna Sani Jabbo, da suka kwashe shekara 48 suna tare, da ya bayyana wa Aminiya yadda lamarin ya faru, ya ce,  “a makon da ya gabata ne da marigayin zai tafi jihar Kebbi daga nan Sakkwato, kamar yadda ya saba, sai ya biya wurin Bello a gidansa, daga nan ne ya gansa da kudi kimanin Naira miliyan biyu, bayan ya tafi  sai  Bello ya kira shi ta waya yake gaya masa ya zo an samu wadansu filaye na sayarwa kuma idan ya saya zai samu alheri sosai. Da margayi ya ji hakan sai y ace wa yaron nasa, ‘bari na turo maka direba,’ sai ya matsa sai dai shi da kansa ya zo.’’  
‘’Da marace bayan an tashi aiki  sai marigayin ya baro Birnin Kebbi zuwa Sakkwato, ko da ya zo gidansa na nan Sakkwato lokacin sallar magariba ta yi, bayan ya kammala sallar ne ya tafi can inda yake kiransa, domin akwai aminci tsakaninsu, kuma gidan da Bello yake da iyalinsa ne, baya tunanin wani abu mummuna, kan haka ya je ba tare da wani tsoro ko shakkunsa ba.’’
Sani Jabbo ya ci gaba da cewa, ‘’Lokacin da ya shiga gidan, ashe yaron ya shirya da wadansu mutum uku a gidan, biyu daga cikinsu ‘yan dambe ne, daya kuma mai shayi ne, dan kabilar Zabarmawa, na karshe dan asalin garin Kwannawa ne,  yana sana’ar wankin babur, kafin zuwan margayin  ya sheda musu  abin da za su aikata, amma sai suka ba shi(Bello) Alkur’ani ya rantse ko asiri ya tonu bayan sun aikata kisan ba zai sanya da su ba, komi runtsi, duk wahala shi kadai zai shiga.”
Ya kara da cewa, “Da zuwansa sai suka sanya shi cikin daki suna bugunsa da saransa da adda da wuka, wadanda ya aro a wurin makwabcinsa. A wannan halin ne marigayi Alhaji ya dauko wayarsa  ya kira direbansa don ya kawo masa agaji, saboda shi ya san gidan Bellon, amma sai suka buge wayar a hannunsa ta fadi kasa, direba sai dai ya rika jin kararsa, amma bai san inda yake da kuma abin da ke faruwa ba.’’
‘’Lokacin da lamarin faruwa matar Bello tana  cikin gidan, da ta ji alamar wani abu na faruwa a daki sai ta garzaya zuwa gidan surukanta ta sheda musu akwai abin da ke faruwa, don ta rika jin karar mutum a dakin kwanan maigidanta har ta yi kokarin shiga amma kofa na rufe. Ko da mahaifinsa ya zo wurin  sun riga sun gama aika-aikarsu. Sai ya samu dansa a kofar gida, da ya tambaye shi sai ya ce masa ai babu komai. Shi mahaifin bai san sun yi wa wannan amini nawa yakan rago, sun nade shi a kwali da buhu da ledar  daki,  sun haka rami a cikin dakin sun bizne shi , suka sake dabe wurin suka sanya tabarma a wurin ba.’’
Da safiyar ranar Alhamis sai iyalin margayin suka kira ni ta waya suna tambayata labarin maigidansu, domin ni ne babban abokinsa da muke waya kullum da safe. Kiransu ne ya ankarar da ni kuskurena, domin tsawon kwanaki biyu abokina bai kira ni ba kuma ni ban bincika me yake faruwa ba. Bayan na gaya musu ban da labarinsa, sai na fara bincikar duk inda yake zuwa amma babu labarinsa. Sai na garzaya zuwa garin Kwannawa,  saboda wannan yaron da direban Alhaji duk a can suke, ko da na zo gidan shi Bellon, sai na samu har iyalan margayi sun kira ‘yan sandan garin sun kama shi, domin suna zarginsa.” A cewarsa.
Gawar Alhaji Yahaya a lokacin da aka dauko ta a gidan Bello Kayan da suka yi amfani da su wurin kashe AlhajiGidan BelloYa ci gaba da cewa, “A ranar Jumu’a muka koma ofishin ‘yan sanda domin cigaba da bincike, a nan ne muka shiga garin domin ko za a samu wani labari, sai Allah Ya gajarce mana wahala wani mutum ya tare mu  ya gaya mana cewa, ‘’wannan yaron da aka kama ya ganshi a kullum yana tayar da wata mota amma bai zuwa da ita ko’ina sai ya kashe ta, a yanzu ma ya sanya mata riga ya rufe ta, amma na san halinku ‘yan sanda, kar ku tona mini asiri, ku bari na shiga gaba duk motar da kuka ga na taba ita ce. Bayan nan sai aka zo da diyar marigayin, tana ganin motar ta tabbatar motar mahaifinta ce. Daga nan aka zo da Bello domin a binciki  gidansa, ana shiga dakin farko sai aka ga jikar Alhaji Yahaya ta kudi amma babu kudin Naira miliyan biyu Da aka tafi daki na biyu aka tarar a rufe, aka ce wannan dakin fa? Ya ce na yara ne, aka ce ina makulli? Ya ce ba nasa ba ne. Nan take daya daga cikin ‘yan sandan ya shuri kofar dakin ya bude, ana shiga sai aka samu takalmin margayi da wani kyalle da jini. dansanda yana kusa da wata tabarma, yana takata sai kawai ya ji ya fada, da alamun akwai rami a wurin. Sai ya ce masa mene ne wannan? Babu wata wahala sai ya ce, ‘’Wallahi Alhaji Yahaya ne muka kashe muka rufe shi a ciki.’’ Daga nan muka dawo hedikwatar ‘yan sanda inda kwamishinan ‘yan sanda ya tambaye shi tare da su waye  suka kashe margayin,  ya ce shi kadai ne, da kyar dai ya fadi sauran wadanda na fadi da farko.’’
‘’Da na tambaye shi laifin me margayi ya yi masa har ya yanke hukuncin raba shi da duniya, sai ya ce babu wani laifi da ya yi masa, kaddara ce kawai ta sanya ya yi haka. Amma a zatona ya kashe shi ne saboda ya mallaki motarsa da Naira miliyan biyu da sauran filaye da gidajensa, wadanda shi kadai ne ya san inda suke, saboda amincewar da marigayin ya yi masa.’’
Kwamishinan ‘yan sanda na jiha r Sakkwato Alhaji Lawal Gambo, ya tabbatar da faruwar lamarin a zantawarsa da manema labarai a gidan yaron da ake zargi da kisan, lokacin da ya ka ziyarar gani da ido.
Ramin da suka turbude Alhaji YahayaKwamishinan ya bayyana cewa, rundunarsu ta samu nasarar cafke mutum shida da ake zargi da kisan, wadanda suka hada da Yanusa Ibrahim da Misbahu Musa da Aliyu Sani da Luba Salihu da Fatima Shehu , suna cigaba da bincike, da zarar sun kammala za su kai su kotu
Marigayi Alhaji Yahaya,  dan shekara 55, ya bar matan aure biyu da ‘ya’ya tara da kuma  jikoki da dama.