Ya kashe wan mahaifinsa ya kone gawar saboda zarginsa da maita
Ya kashe shi sannan ya kona gawar ya binne ta a rami
’Yan sanda a jihar Bauchi sun tsare wani mutum mai suna Haruna Ezekiel saboda zarginsa da kashe yayan mahifinsa mai shekara 80, sannan ya binne shi a cikin wani rami bayan ya zarge shi da maita.
’Yan sandan sun ce an kama matashin mai shekara 35 ne kan zargin kisan Sunday Saleh da ke kauyen Gongo a Karamar Hukumar Tafawa Balewa da ke jihar.
Mutumin dai na zargin tsohon ne da mayar da dansa maye.
Kakakin ’yan sand a jihar, SP Ahmed Wakil, ya ce ofishin rundunar da ke Tafawa Balewa aka kai wa korafin faruwar kisan ranar shida ga watan Disamban 2022, lokacin da wani mazaunin kauyen ya ce ya ga hayaki na tashi a gidan mamacin.
Ahmed Wakil ya ce bayan jami’ansu sun shiga gidan mamacin, sai suka iske cewa wanda ake zargin ya kashe shi, ya kone gawar hade da gidan, kafin daga bisani ya haka rami ya binne shi.
Kakakin ’yan sandan ya kuma ce dan wanda ake zargin ya shaida wa mahaifinsa kwanakin baya cewa wanda aka kashe din ya ba shi wata tsokar nama ya ci inda ya ce masa cin naman alamar shigar da shi maita ce, kuma ana bukatar ya sadaukar da mahaifinsa kafin a kammala yin hakan.
“Da jin haka, sai wanda ake zargin ya fusata ya tunkari mamacin, wanda dama an jima ana zarginsa da maitar,” inji Kakakin ’yan sandan.