Ya kashe ’yar Babban Limamin Bauchi ya binne ta a dakinsa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ta ce ta kama wani matashi mai shekara 30 a duniya bisa zarginsa da kashe wata ’yar Babban Limamin Bauchi Malam Bala Ahmad Baban’inna mai suna Hajara Ahmad.Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi DSP Haruna Muhammed ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 6:00 […]

Ya kashe ’yar Babban Limamin Bauchi ya binne ta a dakinsa
Ya kashe ’yar Babban Limamin Bauchi ya binne ta a dakinsa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ta ce ta kama wani matashi mai shekara 30 a duniya bisa zarginsa da kashe wata ’yar Babban Limamin Bauchi Malam Bala Ahmad Baban’inna mai suna Hajara Ahmad.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi DSP Haruna Muhammed ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 6:00 na yamma, inda wanda ake zargin mai suna Jarelu Ahmad ya ba yarinyar mai shekara 11 guba, bayan ta mutu sai ya binne gawarta a cikin dakinsa.
An kai gawar Hajara Ahmad zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi inda aka gudanar da bincike kuma an gano guba ya ba ta ta sha ta mutu.
Yanzu haka wanda ake zargin yana sashin binciken manyan laifuffuka na hedkwatar ’yan sandan jihar da ke Bauchi ana cigaba da gudanar da bincike.
Sai dai da wakilin Aminiya ya tuntubi Babban Limamin na Bauchi Malam Bala Baban’inna ya ce babu abin da zai ce a yanzu, saboda yana tattaunawa da hukumomin tsaro game da lamarin.