Ya kashe ’yarsa don tana soyayya da Musulmi

Hukumomni a qasar Isra’ila na tuhumar wani Kirista da  kashe ’yarsa da ke soyayya da Musulmi. Jaridar Haaretz ta qasar ta ruwaito cewa ana tuhumar Sami Karra da kashe ’yarsa ’yar shekara 17, mai suna Henriette bayan ta fice daga gidansu da ke tsakiyar birnin Ramle, saboda adawar iyayenta da soyayar da take yi wa […]

Ya kashe ’yarsa don tana soyayya da Musulmi

Hukumomni a qasar Isra’ila na tuhumar wani Kirista da  kashe ’yarsa da ke soyayya da Musulmi. Jaridar Haaretz ta qasar ta ruwaito cewa ana tuhumar Sami Karra da kashe ’yarsa ’yar shekara 17, mai suna Henriette bayan ta fice daga gidansu da ke tsakiyar birnin Ramle, saboda adawar iyayenta da soyayar da take yi wa wani Musulmi.

Matashiyar ta mutu ranar 13 ga Yuni, inda aka sameta da raunuka yankan wuqa a wuya cikin xakin girkin gidan iyayenta. Kamar yadda aka ruwaito ta bar gida ne makonni biyu kafin ta mutu, bayan da iyayenta suka yi barazanar halakata idan ta qi rabuwa da mutumin da rahoton bai ambaci sunansa ba.

Jaridar ta ruwaito cewa mutumin yana zaman kaso a kurkuku, kuma wai Henriette da ta halarci makarantar Yahudawa, ta quduri aniyar shiga addinin Musulunci. Da barin gidansu sai ta voye a gidan mahaifiyar saurayinta. Iyayenta suka ci gaba da yi mata barazana, a wannan karon ma har da mahaifiyar, duk don Henriette ta dawo gida.

Ta xan fake a gidan qawarta. Daga bisani  iyayenta da kawunta suka kai ziyara, inda aka kirawo jami’an ’yan sanda, amma ba su xauki wani mataki ba, saboda Henriette ta nuna bat a buqatar taimako, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Ranar 11 ga Yuni kafin mutuwarta, ’yan sanda da jami’an kula da walwalar al’umma sujn kawo xauki, inda suka gana da iyayen da Henriette. Alamu dai sun nuna sasantawar ba ta yi tasiri ba. Domin tana son zama a gidanta daban, amma dole aka tursasata ta dawo gida, kamar shaidar tabbatar da aikata laifin ta nuna.

Ranar da ta mutu,  ta faxa wa xan uwanta cewa saurayinta zai fito daga kurkuku, kuma tana shirin komawa Musulunci da zarar ya fito. Daga nan sai xan uwanta ya sanar da mahaifinta, wanda ya xauki matakin halaka a gidansu.

Wannan uba dama an tava kama shi da aikata miyagun laifuka, waxanda suka haxa da tsorar da al’umma, amma bai sake kwata laifi ba, tun daga shekarar 2004.

A Isra’ila dama Yahudawa da Larabawa suna samun matsalar wajen soyayya ko auratayya a tsakanin mabiya addinai daban-daban, musamman saboda tashin hankalin da aka shafe shekaru ana yi tsakan Palasxinawa da Yahudawan Isra’ila.

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi