Ya ki barin gidan yari bayan sallamarsa
A makon jiya ne wani fursuna a Jihar Arizona ya ce ba zai fita daga gidan yarin da yake tsare ba, bayan karewar wa’adin zamansa a can, kamar yadda kafar yada labarai ta ABC15.com ta ruwaito a farkon makon nan.Mutumin mai suna, Dabid Spurlock, ya ce zai ci gaba da zama a gidan yarin Maricopa […]
A makon jiya ne wani fursuna a Jihar Arizona ya ce ba zai fita daga gidan yarin da yake tsare ba, bayan karewar wa’adin zamansa a can, kamar yadda kafar yada labarai ta ABC15.com ta ruwaito a farkon makon nan.
Mutumin mai suna, Dabid Spurlock, ya ce zai ci gaba da zama a gidan yarin Maricopa County, bayan an sallame shi ranar Larabar makon jiya. Amma bayan da jami’an gidan yarin suka tilasta masa fita, sai ya fita, ya dawo cikin ’yan sa’o’i.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Presss ya ruwaito, bayan da aka sallame fursunan, dan kimanin shekara 29 da haihuwa, sai ya yi tsalle ya shige motar wani dan sanda a kofar gidan yarin, ya fara kokarin tsere wa da ita. Da aka tambaye shi abin da zai yi da ita, sai ya ce “zai sayar da ita ne.” Daga nan sai aka kara tasa keyarsa zuwa gidan yarin da ya fito bisa zarginsa da sata.
Tun dai da farko an tsare shi saboda laifin ta’ammali da miyagun kwayoyi. Kodayake, ba a kai ga fahimtar abin da ya sa yake shaukin zama a gidan yarin ba tukuna.