Ya koka kan yadda ya iske gidan talabijin din Jigawa
Sabon shugaban gidan talabijin na Jihar Jigawa Alhaji Ishak Hadeja ya koka game da halin da ya samu gidan talabijin din na rashin kayan aiki da rashin iya gudanar da aiki duk da makudan kudin da gwamnatin baya ta ware domin gudanar da harkokinsa.Alhaji Ishak ya fadi haka ne a taron manema labarai da ya […]
Sabon shugaban gidan talabijin na Jihar Jigawa Alhaji Ishak Hadeja ya koka game da halin da ya samu gidan talabijin din na rashin kayan aiki da rashin iya gudanar da aiki duk da makudan kudin da gwamnatin baya ta ware domin gudanar da harkokinsa.
Alhaji Ishak ya fadi haka ne a taron manema labarai da ya kira a gidan talabijin din a ranar Larabar makon jiya, inda ya ce dole shugabannin gidan talabijin din na baya su fito su yi wa gwamnati bayanin yadda suka kashe makudan kudin da aka ba su.
Ya ce gwamnatin Sule Lamido ta kashe sama da naira miliyan 136 domin sayo kayan aiki da bai wa ma’aikata horo amma babu komai a gidan.
Alhaji Ishak Hadeja ya nuna damuwa game da irin abin da ya kira rikon sakainar kashi da shugabanin riko na gidan suka yi wa gidan talabijin din a kankanen lokaci amma bukatar gwamnati ba ta biya ba.
Ya ce duk da cewa sabon gida ne yana bukatar gyare-gyare da samar da kwararrun ma’aikata, inda ya yi alkawarin cewa gidan talabijin din zai bullo da shirye-shirye masu kayatarwa kuma za su hada gwiwa da kamfanoni da ma’aikatun gwamnati don samar masa da kudin shiga da zai iya dogaro da kansa. Ya ce gidan talabijin din zai bai wa kowa damar fadin albarkacin bakinsa babu tare da nuna bambancin siyasa ba.