Ya koka kan yadda yaki ya hana shi auren mata ta hudu

Wani mutum dan Pakistan, mai suna Gulzar Khan ya koka kan yadda farmakin sojoji a yankin Waziristan ya kawo masa cikasa, wajen auren mata ta hudu. Mutumin da ke zaune a Bannu da ke Arewacin Waziristan a kasar Pakistan, ya koka kn yadda ya kashe dimbin tarin kudin da ya ware don auren mata ta […]

Ya koka kan yadda yaki ya hana shi auren mata ta hudu
Ya koka kan yadda yaki ya hana shi auren mata ta hudu

Wani mutum dan Pakistan, mai suna Gulzar Khan ya koka kan yadda farmakin sojoji a yankin Waziristan ya kawo masa cikasa, wajen auren mata ta hudu. Mutumin da ke zaune a Bannu da ke Arewacin Waziristan a kasar Pakistan, ya koka kn yadda ya kashe dimbin tarin kudin da ya ware don auren mata ta hudu, a daidai lokacin da ya ke da mata uku da ’ya’ya 36.
Gulzar Khan, wanda ya samu kansa a cikin daruruwan duban mutanen da suka yi kaura daga yankin na Waziristan, tun bayan da sojoji suka yi ta kai farmaki a sansanonin ’yan Taliban da sauran ’yan tawaye.
Wannan magidanci mai dimbin iyali, ya fice daga gidansa mai dakuna 35 a kauyensu na Shawa, inda akalla magidanta  masu iyali kimanin duibu ke rayuwa da matansu da ’ya’yansu da jikoki.
Magidancin dan shekara 54 yana takaicin yadda ya rika biyan kudin motar kwashe iyalansa dga wannan yanki, alhalin ya ware su ne don auren mace ta hudu.
“Wadannan kudi na tara su ne, amma kwashe iyalina daga Shawa zuwa Bannu ya cinye kudin, yanzu dai na fara tara wasu kudin, inda nike jiran a kamala hare-haren soji,” a cewarsa, lokacin da ya ya yi hira da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
Shari’ar Musulunci dai ta amince mutum ya auri mata har hudu, don haka mutanen Arewa maso Yammacin Pakistan ke da riko da wannan al’ada ta tara dimbin iyali.
Bayan da ya haifi ’ya’ya fiye 12 da kowace mata, sai matansa suka rika nuna masa cewa ya isa haka nan.
 “Ina shirin yin aure na hudu, saboda matana sun turje, inda suka yi mini nuni da cewa a daina haihuwar ’ya’ya haka nan,” inji Khan.
Khan dai yana da shekara 17 ya auri diyar kawunsa ’yar shekara 14, a kauyensu na Shawa. Sun haifi ’ya’ya mata takwas da maza hudu, amma bayan shekara takwas, sai wannan gwarzo ya sake auren wata matar ’yar shekara 17.
Maigida Khan yana da gida mai dakuna 17 da ke Arewa maso Yammacin Bannu, inda mafi yawan wadanda yaki ya kora suke gudun hijira. Ya yi tukin tasi a masarautar Dubai da ke cikin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), a tsakanin shekarun 1976 zuwa 1992.
Wannan dattijo ya auri matar dan uwansa da ya mutu, a amtsayin mata ta uku, bayan an kashe shi, wata guda da yin aurensu.
Biyu daga cikin ’ya’yan gulzar Khan direbobi ne da ke aiki a Dubai, kuma suna turo masa kudi, don tallafa wa iyalansa, inda yake hadawa da kudin da yake samu daga noman da yake yi a gonakinsa da ke Bannu da Shawa.
“’Ya’yana na aiko mini da Rupees dubu 50, wato kimanin Dala 500 daga Dubai a kowane wata, kuma muna amfani da kudin wajen biyan bukatun yau da kullum,” a cewar Khan.
Ya ce babu wata hatsaniya ko tashin hankali a tsaknin matansa, duk suna zaune a gida guda, amma ya tabbatar da cewa, yana shan fama wajen tunanin yadda zai tantance ’ya’yan wance da na wance.
“Zan iya gane wannan ko waccan (yaro ko yarinyar) da ko ’yata ce, amma ba zan iya tantance wace ce mahiafiyarsa ko mahaifiyarta.,” inji Khan.
Al’adar mutanen wannan yanki t ahana matan aure Magana da mutanen da ba a cikin iyalinsu suke ba, don haka wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na AFP bai wsmau tattaunawa da daya daga cikin matan Khan ba.
Maigida Khan ya ce ba ya samun matsala wajen ciyarwa da tufatar da iyalajnsa, amma yawan mutanen gidansa na sanyawa ba shi da sirri.
“”Kusan kodayaushe akwai yara biyu ko uku da ke kwanciya kusa da ni idan na tafi kwanciya, don haka ina samun matsa wajen kebewa da matana,” inji Khan.
“Na taba yin fama\ da ciwon zuciya da gyambon ciki, shekara 12 da ta wuce, sai likitana ya shawarce ni kan cewa lallai in kasance cikin farin ciki,” a cewarsa, kamar yadda ya bayyana wa AFP.
Asusun Kula da Yawan Al’umma na Majalisar dinkin Duniya, ya yi nuni da cewa yawan mutanen Pakistan da yakai miliyan 180, bisa kididdigar shekarar 2012, ya yi nuni da cewa daya bisa uku na mutanen Pakistan ba su samu magungunan tazarar haihuwa. Wasu masu nazarin al’amura, sun nuna cewa albarkatun kasar sun yi al’ummar kadan.
Shi kuwa daya daga cikin ’ya;yan Khan, dan shekara 14, mai suna Ghufran ba shi da wata fargaba. “In Allah Ya yarda zan yi aure-aure, in haifi ’ya’ya fiye da mahaifina,” inji shi, a hirar da ya yi da AFP.