Ya kona dansa saboda satar Naira 500

‘Yan sanda sanda sun kama wani magidanci mai suna Idorenyin Essien, da ya kona dansa a garin Afia Nsit Karamar Hukumar Eket a jihar Akwa Ibom. Idorenyin, mai shekara 35 da ake zargin ya yi sanadiyyar mutuwar dansa ta hanyar kona shi, bayan ya samu labarin cewa dan nasa ya saci Naira 500 a gidan […]

Ya kona dansa saboda satar Naira 500

‘Yan sanda sanda sun kama wani magidanci mai suna Idorenyin Essien, da ya kona dansa a garin Afia Nsit Karamar Hukumar Eket a jihar Akwa Ibom.

Idorenyin, mai shekara 35 da ake zargin ya yi sanadiyyar mutuwar dansa ta hanyar kona shi, bayan ya samu labarin cewa dan nasa ya saci Naira 500 a gidan makwabcinsa ya sayi abinci.

Daya daga cikin shugaban unguwar Afia Nsit, mai suna Effiong Okon, ne ya sanar da hakan ya ce Idorenyin, ya kona dansa ne bayan ya daure sai ya kunna masa wuta.

Idorenyin, ya mayarwa da makwabcinsa Naira 500 da dansa ya sata, sannan ya aika yaron siyan kalanzir kafin ya kona shi.