Ya kona matarsa don tana haifar masa mata

Ga alama tsugunni-tashi ba ta kare wa wani magidanci mai suna Paul a Jihar Ebonyi ba sakamakon babbaka matarsa da ya yi sabili da tana yawan haifa masa ’ya’ya mata. Aminiya ta ruwaito cewa wanda ake zargi ya hada baki da wasu matasa zauna-gari-banza da ake wa lakabi da ‘eriya boyiz’ ya biya su awalaja […]

Ya kona matarsa don tana haifar masa mata
Ya kona matarsa don tana haifar masa mata

Ga alama tsugunni-tashi ba ta kare wa wani magidanci mai suna Paul a Jihar Ebonyi ba sakamakon babbaka matarsa da ya yi sabili da tana yawan haifa masa ’ya’ya mata.
Aminiya ta ruwaito cewa wanda ake zargi ya hada baki da wasu matasa zauna-gari-banza da ake wa lakabi da ‘eriya boyiz’ ya biya su awalaja mai tsoka suka faki matarsa mai suna Monica Nwanpuken suka watsa mata fetur suka kunna mata wuta.
 Paul, wanda ake zargi da kona matarsa na da kantin saida magunguna a kauyen Onuojgon da ke karamar Hukumar Ikwo ta Jihar Ebonyi, ya yi wa jami’an tsaro bayanin shi ne ya sanya matasan yi wa matarsa haka, saboda shi namiji yake so matarsa ta rika haihuwa, amma sai ta buge ga haifar ’ya’ya mata, abin da ya bakanta masa rai ke nan ya dauki doka a hannunsa.
Sunday Nwigbo, kanen matar da aka kona, a bayanin da ya yi wa Aminiya ya ce, “Paul tun shekara goma sha biyu da suka gabata ne ’yar uwarsa na makarantar sakandare ya yi mata ciki suke zaune take haifa masa ’ya’ya mata, lamarin da ya rika jefa rudani da zaman dar-dar da kyarar juna tsakaninsa da matarsa har ya dauki waccan doka a hannunsa.”
Monica dai yanzu haka tana asibitin gwamnatin tarayya ana jinyarta.
Wakilinmu ya tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Ebonyi Chris Anyawu game da lamarin, sai ta ce, “Abun da zan iya ce maka, mu ba mu samu labarin wani abu makamancin haka ba, amma idan mun samu zan sanar da kai”.