Yadda wani ya yi kwanaki makale a ramin hakar gwal
An kubutar da wani mutum bayan ya shafe kwana biyu makale a tsohon ramin hakar ma’adanai a lokacin da ya je don neman gwal. John Waddell, dan shekara 60 ya shaida wa abokinsa cewa idan har bai dawo gida a ranar Talata ba, a je a dubo shi. An gano inda yake a ranar Laraba bayan […]
An kubutar da wani mutum bayan ya shafe kwana biyu makale a tsohon ramin hakar ma’adanai a lokacin da ya je don neman gwal.
John Waddell, dan shekara 60 ya shaida wa abokinsa cewa idan har bai dawo gida a ranar Talata ba, a je a dubo shi.
An gano inda yake a ranar Laraba bayan bacewar tasa.
Mutumin dan Jihar Arizona na kasar Amurka ya fita don neman gwal ne a wani yanki mai hamada, inda ya fada wani katon rami mai tsawon kafa 100, al’amarin da ya jawo aka shafe lokaci mai tsawo kafin a samu damar kubutar da shi.
John, ya fada cikin ramin ne a daren Laraba, kwana biyu kafin igiyoyin da suke rike da shi su tsinke, inda ya makale a tsakiyar ramin yana tangal-tangal a tsakanin kafa 40 zuwa 50 a cikin ramin.
Terry Shrader ya ce Waddell, abokinsa ne na kusa.
“Ya kira ni ranar Litinin, ya shaida min cewa ya yi tattaki zuwa wani yanki mai hamada kusa da Aguila, tafiyar mil 90 daga Arewa maso Yammacin Phoenid, da niyyar neman karafan zinare”, inji abokinsa.
Mahukunta a ranar Laraba sun tabbatar da cewa Waddell shi ne ya mallaki kayan hakar ma’adanai da suke yankin sannan ya shafe shekara 20 yana gudanar da wannan aiki.
Waddell da abokinsa sun yi yarjejeniyar idan har ba a gan shi ba ranar Talata, to lallai a tafi domin lalubo shi.
Shrader ya fada wa kafar watsa labarai ta NBC cewa ya damu matuka a lokacin da Laraba ta yi ba tare da ya ji duriyar abokinsa ba. Sa’ar da aka ce shi ne ya san inda abokin nasa ya je.
Ya ce “a lokacin da na sauko daga mota ‘a kori kura’ na jiwo shi yana ihu”, inji Shrader.
Ya ce “sai na nemi inda zan samu damar kiran waya, na kira lambar neman agaji ta 911. Sannan na tura wa Waddell ruwa kafin masu kawo agaji su karaso”,
An shafe sa’o’i biyar kafin a samu damar ciro Waddell, an yi amfani da na’o’rar daukar bidiyo a lokacin da ake kokarin ceto shi daga ramin.
An garzaya da shi zuwa cibiyar lafiya ta Banner-Unibersity Medical Center da ke Phoenid.
Ya samu raunuka masu hadari kamar yadda jami’in ’yan sandan yankin ya rubuta a shafinsa na Twitter.
Asibitin da ke kula da Waddell ya shaida wa NBC cewa ya samu karaya a kafarsa sannan an shiga da shi dakin tiyata a ranar Alhamis.
Mista Waddell yana cikin farin cikin sake kasancewa tare da masoyansa inda yake samun murmurewa.