Ya kubuta daga hannun masu garkuwa da tabon harsashi a jikinsa

Daya daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su da yammacin ranar Lahadi a Jihar Neja ya tsallake rijiya da baya.

Ya kubuta daga hannun masu garkuwa da tabon harsashi a jikinsa

Motar Fasinja da yan bindigar suka kai wa hari

Daya daga cikin fasinjoji 18 da aka yi garkuwa da su da yammacin ranar Lahadi a Jihar Neja ya tsallake rijiya da baya.
Rahotanni sun ce mutumin ya kubuta ne daga hannun masu garkuwar da harsashi a jikinsa.

Masu garkuwar dai sun yi garkuwa da mutane 18 daga cikin 21 dake motar kirar Safa mallakar Hukumar Sufuri ta Jihar (NSTA).

Wata mata tare da yaronta ne kadai suka sami kubuta kafin daga bisani kuma a kawo mata dauki.

Lamarin ya ritsa da fasinjojin ne a kan hanyar Tegina zuwa Zungeru dake jihar ta Neja a ranar lahadi.
Yanzu haka mutumin da ya kubuta daga hannun masu garkuwar yana samun kulawar jami’an lafiya a wani Asibiti da ba’a bayyana sunansa ba saboda ya samu kariyar da ta dace da shi.