Ya maka matarsa a kotu kan zargin cutar kanjamau
Yau Juma’a ne za a ci gaba da sauraron karar da wani magidanci ya kai matarsa da iyayenta Kotun Fagge Waje bisa zargin da kai masa cikin da ba nasa ba, kuma tana dauke da cutar kanjamau. Magidancin mai suna Nazifi Balarabe dandinshe ya shaida wa kotun cewa bai dade da auren matarsa Bilkisu ba, […]
Yau Juma’a ne za a ci gaba da sauraron karar da wani magidanci ya kai matarsa da iyayenta Kotun Fagge Waje bisa zargin da kai masa cikin da ba nasa ba, kuma tana dauke da cutar kanjamau. Magidancin mai suna Nazifi Balarabe dandinshe ya shaida wa kotun cewa bai dade da auren matarsa Bilkisu ba, amma sai ya ga tana dauke da ciki wata bakwai, kuma a asibiti an shaida masa cewa tana da cutar kanjamau. Magidancin ya shaida wa kotun cewa bayan an yi masa gwaji a asibiti, likitoci sun ce yana wani mataki da cutar za ta iya zama babba a jikinsa a kowane lokaci daga yanzu. Ya ce dan uwan matarsa mai suna Alhaji Muhamamd Ra’is ne ya aurar masa da ita duk da yana sane da cewa ’yar uwar tasa tana da cutar da kuma juna biyu, don haka ya nemi kotun ta tilasta wa wadanda yake kara su biya shi dukkan kudin da ya kashe a lokacin aurensu da matar. Sai dai Bilkisu ta musanta zargin da mijin yake yi mata, inda ta ce ta je asibiti don yin gwajin cutar kanajmau sai dai har zuwa lokacin ba a ba ta sakamakon gwajin ba. Kuma ta ce cikin da ke jikinta na mijinta ne. Alkalin kotun Mai shari’a Abdu Abdllahi Waiya ya dage sauarn shari’ar zuwa yau Juma’a don bayar da dama ga bangarorin su kawo shaida kan da’awarsu.