Ya makure abokinsa a kan Naira dubu 40

Al’ummar Unguwar kofar Kudu a yankin karamar Hukumar Tofa cikin Jihar Kano suna ci gaba da alhinin rasuwar dan uwansu mai suna Muzammil, Hamisu wanda aka fi sani da dan asabe, sakamakon kashe shi da ake zargin wani abokinsa ya yi kimanin makonni biyu da suka gabata. Lamarin mai kama da almara ya samo asali […]

Ya makure abokinsa a kan Naira dubu 40

Al’ummar Unguwar kofar Kudu a yankin karamar Hukumar Tofa cikin Jihar Kano suna ci gaba da alhinin rasuwar dan uwansu mai suna Muzammil, Hamisu wanda aka fi sani da dan asabe, sakamakon kashe shi da ake zargin wani abokinsa ya yi kimanin makonni biyu da suka gabata.

Lamarin mai kama da almara ya samo asali ne watanni uku da suka gabata inda Marigayi Muzammil (dan Asabe) mai kimanin shekaru 24 da haihuwa, wanda ke gudanar da sana’ar kafinta, ya dauki kudinsa Niara dubu 40 ya ba wa abokinsa mai suna Hamisu Mijinyawa don ya saya masa kalwa, kasancewar Hamisun yana gudanar da sana’ar sarin kayan abinci da sauransu.
Rahotanni sun bayyana cewa, tun daga wanacan lokaci da Hamisu ya karbi kudin dan Asabe ya kwanta a kansu ba tare da ya yi masa bayanin halin da ake ciki ba. Lokacin da dan Asabe ya gaji da zura wa abokin nasa ido sai ya yi masa magana, inda shi kuma Hamisun ya gaya masa cewa mutuimn da zai kawo masa wasu kaya ne har yanzu bai kawo ba.
Aminiya ta gano cewa, matsantawar da dan Asabe ya yi wa abokin nasa game da son karbar kudin nasa ne ya jawo ya dauki matakin kashe shi, inda ya tafi da shi bayan gari ya kashe shi ta hanyar shake masa wuya, bayan ya mutu ya samu wuri cikin daji ya rufe gawar da kayoyi ya dawo cikin gari ya ci gaba da harkokinsa.
Lokacin da iyaye da ’yan uwan dan Asabe suka farga da bacewarsa, Hamisu yana daga cikin mutane na farko da aka fara nema don bin bahasi, sai dai da farko ya nuna ba shi da masaniya game da bacewar abokin nasa. Asirin wanda ake zargin ya tonu ne bayan kwanaki 12 da bacewar dan asabe, sakamakon tashin wata ‘yar rigima tsakaninsa(Hamisu) da wani dan dako mai suna Dini, inda Dinin ya nemi Hamisu ya biya shi wasu kudin aikinsa amma ya hana shi.
Lokacin da Dinin ya fara damunsa da maganar ne, Hamisun ya yi ikrarin cewa idan bai kyale shi ba zai yi masa abin da ya yi wa dan Asabe. Jin lafazin da Hamisu ya furta ya sa Dini ya je gidan su marigayi dan Asabe ya sanar da ‘yan uwansa.Daga nan ne iyayen marigyin suka sanar da ‘yan sanda halin da ake ciki, inda suka kama Hamisu suka shiga bincike, har dai a karshe bayan ya sha wuya ya amsa laifinsa, tare da nuna musu wurin da ya boye gawar marigayin, wacce tuni ta fara zagwanyewa.
Mafi yawan jama’ar garin Tofa sun bayyana marigayi dan Asabe a matsayin matashin kwarai wanda babu ruwansa da shiga riginmgimu. Haka kuma sun bayyana shi a matsayin mutum mai kwazon neman abin kansa.
Tuni dai aka yi jana’izar marigayi dan Asabe kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Malama Mairo Hamisu ita ce mahaifiyar marigayi dan Asabe, ta bayyana cewa a lokuta da dama dan nata ya sha yi mata batun makalewar kudinsa a hannun abokin nasa, sai dai takan ba shi hakuri da cewa tunda akwai abota a tsakaninsu ya kamata ya bi komai a hankali. “Tun daga lokacin da ya fahimci yawo da hankalin da abokin nasa Hamisu yake yi masa game da kudin, yakan yi min batun cewa yana son ya amshi kudinsa, to ni kuma a koyaushe nakan yi masa nasiha da ya bi komai a hankali. A ranar da lamarin zai faru sai ya gaya min cewa abokin nasa Hamisu ya nemi ya je ya karbo kalwarsa, ni kuma daga nana muka yi salalma na tafi gidan biki. Da dare ya yi na dawo ban ga dan Asabe ya shigo gida ba, har na yi barci. Da safe da na tashi ma ban gan shi ba. Sai na shiga dakin da yake kwana na ga shimfidarsa a jingine. Hakan ya tabbatar min bai kwana a gida ba, abin da bai taba yi ba. Nan da nan sai batun karbo kalwa ya fado min, na shiga tunanin to me zai sa daga dauko kalwa wanda a cikin gari gidan yake, amma har ya tafi ya kwana. Nan dai muka fara nemansa, muka aika aka nemo abokin nasa, wanda dama tare suka tashi tun da aka haife su. Da ya zo sai ya ce wai sun hadu amma bai dauki kalwar ba, sai dai sun je wata Unguwa inda kuma ya sauke marigayin a bakin kwalta ya wuce gida. Daga nana ba mu sake bi ta kansa ba, sai muka ci gaba da cigiya tare da addu’a don neman bayyanar dan Asabe, ba tare da sanin cewa tuni an riga an kashe shi ba,” inji ta.
Mahaifiyar dan Asabe ta bayyana cewa, kasancewar mahaifin dan Asabe ya rasu kimanin shekaru hudu da suka gabata, ba karamin kudi ta raba wa malamai ba don yin addu’ar bayyanar marigayin. “Zan iya cewa na kashe kudi ya fi Naira dubu 50.” Inji ta.
Kakakin Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya, ya tababtar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa wanda ake zargin yana hannunsu, tuni kuma ya amsa laifin da ake zarginsa da shi.’’
Bayan da lamarin ya faru jami’anmu da ke garin Tofa sun kama wanda ake zargin inda ya amsa laifinsa tare da bayyana yadda ya kashe marigayin, inda ya ce ya yi amfani da igiya ne ya shake wuyan marigayin har sai da ya mutu. Bayan wanda ake zargin ya nuna wurin da ya rufe gawar marigayin an dauko ta an kuma yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A yanzu haka wanda ake zargin yana sashen binciken manyan laifuka da ke hedikwatar rundunar ’Yan sanda ta Bompai. Da zarar mun kammala bincike za mu gurfanar da shi gaban kuliya don tuhumarsa da laifin kisan kai, wanda ya saba wa sashe na 221 na dokar pinal kod,” inji Majiya.