Ya mayar da danyar kaza abincinsa

Ya zamar masa kamar al’ada, inda yake cin danyen nama duk rana.

Ya mayar da danyar kaza abincinsa

Blazen yana cin danyen naman kaji

Wani mutum mai suna Blazen ya wallafa bidiyonsa don ya tabbatar wa duniya cewa yana cin naman danyar kaza a matsayin abincin da yake kauna.

Mutumin mai wasan motsa jiki, ya janyo cece-kuce bayan ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Twitter mai adireshin @BlazenBrady.

A bidiyon da Blazen ya wallafa, ya nuna yadda yake cin danyan naman kaji wadanda aka yi wa musu gunduwa-gunduwa ta tsokar nama.

Ya ce, yana cin abincin bayan kowane motsa jiki da ya yi, ya nanata kara jin dadin kajin da yake ci danyu kuma ya tabbatar da dandanon kajin da yake ci.

Amma mutane ba su amince da gaske cin danyen naman kaji yana daga cikin abincinsa ba.

Don haka, ya tabbatar musu da gaskiyar lamarin, sai Blazen ya dauki bidiyon kansa lokacin da yake cin danyar kaza a zahiri.

Ya ce: “Ba wai abu ne mara kyau ba, mutane suna ta ceceku-ce kan wannan lamari.”

A cikin bidiyon, ya ce: “Da kyau, na samu mutane da yawa suna neman na yi wannan bidiyon, saboda wadansu mutane ba su yarda ina cin kaza danya ba.

“Ba wani abu ba ne mara kyau, ku daina cece-ku-ce kan cin danyar kazar,don ina tunanin wadansu na fargaba saboda kawai an bayyana muku cewa, ana iya kamuwa da wasu kwayoyin cuta a ciki.

“Abincinku ne na asali, kuma ni ina son cinsa a zahiri yadda yake danyensa.

“Babu wani bambanci a dandanonsa kuma wannan ba abin mamaki ba ne, amma ba ya dandano mai dadi idan an dandana.

“Sai dai ya zamar mini kamar al’ada don kuwa ina cinsa duk rana.

“Nakan wanke shi da madara don in saba da shi lokacin da na fara, yanzu ya ya zame min jiki.

Sai dai masana sun yi gargadi game da cin danyar kaza ko wanda ba a dafa ba saboda yiwuwar kamuwa da kwayoyin cuttuttuka da za su iya haifar da guba a abinci da sauran cututtuka masu tsanani.

Haka kuma, mabiya shafukan Twitter suna ta zolayar abincin Blazen, inda wani mai amfani da shafin ya wallafa: “Ba zan ma iya ciyar da wannan naman ga karena ba. Ka kula da kanka.”

Wani kuwa sharhi ya yi a shafinsa na Twitter mai adireshin @SLAYZUR: “Wannan man shanu ne yana rufe jijiyoyinku yayin da hakan ke janyo muhawara.”

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’