Ya mayar da rigarsa tsumma bayan United ta doke Arsenal

Wani abin dariya ya faru a Ingila bayan mai goya wa kulob din Arsenal baya ya kekketa rigarsa ta gaba da ta baya saboda nuna bacin ransa a kan dokewar da kulob din Manchester United ta yi wa Arsenal da ci 3-2 a ranar Lahadin da ta gabata a gasar rukunin firimiya na Ingila.An ce […]

Ya mayar da rigarsa tsumma bayan United ta doke Arsenal
Ya mayar da rigarsa tsumma bayan United ta doke Arsenal

Wani abin dariya ya faru a Ingila bayan mai goya wa kulob din Arsenal baya ya kekketa rigarsa ta gaba da ta baya saboda nuna bacin ransa a kan dokewar da kulob din Manchester United ta yi wa Arsenal da ci 3-2 a ranar Lahadin da ta gabata a gasar rukunin firimiya na Ingila.
An ce labarin ya yadu ne bayan mutumin ya baza hoton rigarsa da ya yi wa kacaca a shafin abota na facebook don nuna wa duniya halin da yake ciki.
Idan za a tuna, a ranar Lahadin da ta wuce ne kulob din Manchester United ya lallasa na Arsenal da ci 3-2 bayan matashin dan kwallon United Rashold ya zura kwallaye biyu kuma ya taimaka wajen zura ta uku a ragar Arsenal. Hakan ta sa kulob din Leicester City ya ba na Arsenal tazarar maki biyar kuma a lokacin ana saura wasanni 11 a kammala gasar.
Rahoton ya ce mai goyon bayan kulob din ya harzuka ne jim kadan bayan an tashi wasan inda ya yayyaga rigarsa gaba da baya, ya mayar da ita tsumma kuma ya dauki hotonta ya watsa a shafinsa na facebook tare da fadin bakaken maganganu, duk a kokarinsa na nuna bacin ransa.
Bayan ya kacaccala rigar tasa ce inda ya cire wuya da hannu da kuma kirji da baya, sai ya nemi mai bukatar saye.  Yin haka tamkar cin fuska ne ga kulob din Arsenal kuma zagi ne a fakaice ga mahukunta kulob din da kuma ’yan kwallonsa.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa