Ya mutu a dakin karuwa ana dab da bikinsa
Wani direban tankar mai ya gamu da ajalinsa yana tsaka zina a dakin karuwa a wani hotel da ke yankin Oluti a unguwar Festak a Legas. Direban mai shekara 32 da ke aiki da wani kamfanin man fetur a yankin Ajah a Legas ya je da motarsa defot daukar man fetur ne a yankin Ijegun, […]
Wani direban tankar mai ya gamu da ajalinsa yana tsaka zina a dakin karuwa a wani hotel da ke yankin Oluti a unguwar Festak a Legas.
Direban mai shekara 32 da ke aiki da wani kamfanin man fetur a yankin Ajah a Legas ya je da motarsa defot daukar man fetur ne a yankin Ijegun, sai ya nufi wata mashaya tare da abokansa direbobi da misalin karfe 10 na dare.
Bayan ya gama shan giya a mashayar ne ya hadu da wata karuwa da ke aiki a hotel din da ke jikin mashayar, ya daidai ta da ita suka je dakinta inda ajali ya riske shi a ciki.
Karuwar da direban ya mutu a dakinta, mai shekaru 24, ta shaida cewa yana kan saduwa da ita ne ya fita daga hayyacinsa, kafin daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa a asibiti.
Ta ce ya tunkare ta bayan ya kammala shan barasa inda ta bukaci ya ba ta naira dubu goma, sai ya nemi ragi ya bata naira dubu bakwai.
“Muna shiga dakin ya sadu da ni a karon farko, sai muka yi barci muka huta, da misalin karfe 2:30 na dare sai ya tada ni daga barci ya bukaci ya sake saduwa da ni.
“Yana tsaka da saduwa da ni a karo na biyu ne sai na lura numfashinsa ya fara daukewa, daga nan ya fita hayyacinsa.
“Ganin haka ne ya sa na kurma ihu domin nema masa agaji”, inji ta.
Ta kara da cewa manajan hotel din ya zo bayan da ya ji ihunta inda suka garzaya da direban wani asibiti mai zaman kansa a yankin.
Daga can sai aka nemi su kai shi Babban Asibitin Mainland da ke Yaba, sai dai ba da jimawa ba ya mutu a asibitin.
Jami’an rundunar ‘yan sanda da ke binciken miyagun laifuka (CIID) na yankin Panti a Yaba na binciken lamarin yayin da suke ci gaba da tsare karuwar domin tatsar bayanai daga gare ta.
Direban dan asalin jihar Edo ya gamu da ajalinsa a dakin karuwa ne a daidai lokacin da ake shirin bikin aurensa cikin kasa da wata guda (watan Satumba).
An samu buhu biyu na shinkafa da ya tanada domin bikin auren nasa.