Ya mutu a lokacin da yake kwallo a Ajantina
A ranar Lahadin da ta wuce ne wani abin al’ajabi ya sake faruwa a Ajantina bayan wani dan kwallo mai suna Cristian Gomez ya fadi bayan sun yi arangama da wani dan kwallo kuma nan take ya sheka barzahu kafin a kai shi asibiti. Wannan shi ne karo na biyu da hakan ke faruwa a […]
A ranar Lahadin da ta wuce ne wani abin al’ajabi ya sake faruwa a Ajantina bayan wani dan kwallo mai suna Cristian Gomez ya fadi bayan sun yi arangama da wani dan kwallo kuma nan take ya sheka barzahu kafin a kai shi asibiti. Wannan shi ne karo na biyu da hakan ke faruwa a kasar, bayan wanda ya faru a ranar 14 ga watan nan da muke ciki ga wani dan kwallo daban, inda shi ma ya yanke jiki ya fadi matacce bayan ya yi arangama da kai da wani kankare da ke bayan filin da suke kwallo. A wancan karo, wani dan kwallo ne mai suna San Martin Burzaco ya mutu bayan ya yi taho-mu-gama da kai inda ya hadu da wani kankare da ke bayan fili bayan ya yi kokarin tare kwallo al’amarin da ya sa ya nan take ya sume kuma duk kokarin da aka yi don ya farfado abin ya ci tura, daga karshe Likitoci suka bayar da tabbacin mutuwarsa bayan sun yi masa gwaje-gwaje a asibiti.
Hakan ta sa aka dage gasar da tsawon makonni biyu, sai ga shi a karo na biyu a kasa da makonni uku an sake kwatawa.
Shi dai Cristian Gomez, dan wasan baya ne a kulob din Atletico Parana da ke wasa a gasar rukuni-rukuni ajin ’yan dagaji da aka kira Primera B kuma sun yi wasan ne da kulob din Boca Unidos. Ya fado kasa a sume ne bayan ya yi arangama da dan kwallon Boca Unidos a kokarin da kowanensu yake na dauke kwallo da kai, amma suka yi arangama, nan take suka watse warwas a kasa amma shi Gomez ko shurawa bai yi ba yayin abokin karawarsa ya tashi babu ko kwarzane. Nan take takwarorinsa da ke filin suka yi caa a kansa suna masa fifita da kururuwar a kai masa dauki. Nan da nan aka garzaya da shi asibiti mafi kusa amma a can ne Likitoci suka tabbatar da mutuwarsa bayan sun yi gwaje-gwaje a kansa.
“A lokacin da yake sume, takwarorinsa da ke filin kowa ya tube rigarsa inda suka rika yi masa fifita da kururuwar neman taimakon gaggawa, amma ina, kafin kankanen lokaci rai ya yi halinsa”, inji Miguel Darre Likitan Boca Unidos kungiyar da ta fafata da ta marigayin a lokacin da yake hira da manema labarai.
Shi kuwa jami’in da ya lura da yadda wasan ya gudana (Match superbisor) mai suna Ramon Gomez ya bayyana al’amarin a matsayin takaici. Ya ce babu wanda ya taba tsammanin irin haka za ta sake faruwa amma dai babu abin da za su iya yi sai yi wa mamacin addu’a.
Tuni kulub din marigayi Gomez da na Boca Unidos suka aika sakonninsu na ta’aziyya ga iyalan mamacin.