Ya nemi kotu ta raba aurensa saboda matarsa na haihuwa

Wani magidanci mai shekara 56 ya nemi kotu ta raba aurensa da matarsa, saboda tana haihuwa duk shekara.

Ya nemi kotu ta raba aurensa saboda matarsa na haihuwa

Ma’aurata

Wani magidanci mai shekara 56 ya nemi kotu ta raba aurensa da matarsa, saboda tana haihuwa duk shekara.

Magidancin ya ce bai taba tunanin matar za ta haihu ba, amma cikin shekara shida da suka yi aure sai ga shi ta cika mishi gida da yara.

Ya shaida wa kotun cewa, “A tunanina shi ne za mu samu farin ciki da juna, ba wai ta zo ta cika min gida da kananan yara ba.”

Ya ce matar tasa da ya aura bayan rasuwar matarsa ta farko masifaffiya ce, ga raini, sannan ba ta son mutane.

Hakan ne ma ya amsa, “Babban dana daga tsohuwar matata ya bar gidan saboda yadda take yawan rikici da shi;

“Sauran yaran maza biyu ma sun bar gidan — a kan dan kankanin abu sai kawai ta fara zagin su.

Amma matar ta musanya zargin, tana mai cewa yaudarar ta mijin nata ya yi ya aure ta.

Ta ce, “Bai taba gaya min cewa ba ya son mu haihu da shi ba, kuma kafin ya aure ni yana sane cewa ina  da ’ya’ya hudu da tsohon mijina ya rasu ya bari.

“Ya yi alkawarin ba ni kulawa tare da ’ya’ya nawa amma ashe karya yake yi.

“A 2018 na fara daukar cikinsa kuma haifi da mai lalura; mijin nawa na zuwa ya yi ido hudu da jaririn ya ce ga garinku nan.

“Bayan na dauki ciki ya ba ni wata ƙwayar, ban san ashe na zubar da ciki ba ne.

“Sai da na yi sati biyu ina zubar da jini kuma cikin ya zube; daga baya ya shaida min cewa abin kunya da tsufarsa a ga matarsa ta haihu.

“Ya ce ya auro ni ne kwai domin ya rika kwanciyar aure da ni, ina masa wanki da girki da kula da shi, amma na shaida mishi cewa ba za ta sabu ba, mene ne ribar aure idan babu haihuwa.’’

Bayan sauraron bangarorin, shguaban kotun, Koledoye Adeniyi, ya dage shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Yulin da muke ciki.