Ya nemi a yi wa bangaren ilimi garambawul

Wani fitaccen masani kuma malami a Jami’ar Abuja, Dokta Gabardeen Olubenga Wasiu, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi wa bangaren ilimi garambawul tun daga matakin farko.Dokta Wasiu wanda har ila yau shi ne Shugaban Tsangayar Ilimi ta Jami’ar Abuja, ya yi kiran ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya, inda ya ce, “Halin […]

Ya nemi a yi wa bangaren ilimi garambawul
Ya nemi a yi wa bangaren ilimi garambawul

Wani fitaccen masani kuma malami a Jami’ar Abuja, Dokta Gabardeen Olubenga Wasiu, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi wa bangaren ilimi garambawul tun daga matakin farko.
Dokta Wasiu wanda har ila yau shi ne Shugaban Tsangayar Ilimi ta Jami’ar Abuja, ya yi kiran ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya, inda ya ce, “Halin da ilimi ya shiga yana bukatar a yi masa garambawul kuma muna bukatar mu kira wadanda suke da sha’awa a bangaren su zo su bayar ta tasu gudunmawar don nemo hanyoyin da za a warware matsalolin da ke fuskantar ilimi a Najeriya.”
Ya ce wannan ne hanyar da za a magance kalubalen da ke fuskantar ilimi a Najeriya.
Dokta Wasiu ya ce gwamnati ta dade tana bai wa sashin manyan makarantu fifiko wanda a ganinsa haka ya sanya ilimin makarantun firamare ya tabarbare. Ya ce sai gwamnati ta dawo ta gyara ilimi tun daga tushe ta hanyar daukan matakan da suka dace sannan za a magance matsalolin da ake addabar bangaren.
Ya bayyana takaicinsa kan yadda ’yan Najeriya suka mayar da batun ilimi tamkar gugar yasa, inda ya ce mutane suna shiga harkar ilimi ba tare da samun kwarewar da ta dace ba. “Babu inda mutane suke yi wa kutse irin bangaren ilimi. Kuma da yawa daga cikinsu suna shiga harkar ne idan suka rasa aikin yi ba tare da samun wata kwarewa ta musamman ba. Wannan abin takaici ne don in ban da bangaren ilimi babu inda mutane suke yin kutse kai-tsaye,” inji shi.