Ya nemi gwamnati ta saukaka wa Musulmi aikin Hajji
An yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta bullo da tsare-tsare masu inganci da za su sanya Musulmi su samu saukin gudanar da aikin Hajji a kasa Mai tsarki. Shugaban Daraktocin Gidan Talabijin na Manara kuma Shugaban kungiyar Izala ta kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya yi kiran yayin da yake tattaunawa da manema labarai […]

An yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta bullo da tsare-tsare masu inganci da za su sanya Musulmi su samu saukin gudanar da aikin Hajji a kasa Mai tsarki.
Shugaban Daraktocin Gidan Talabijin na Manara kuma Shugaban kungiyar Izala ta kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya yi kiran yayin da yake tattaunawa da manema labarai bayan kammala taron tattaunawa kan aikin Hajji da gidan talabijin din ya shirya a Abuja, a karshen makon jiya.
Sheikh Bala Lau ya ce Gidan Talabijin na Manara ya shirya tattaunawa a kan aikin Hajji ne don bayar da gudunmawarsa a matsayinsa na Gidan Talabijin mai yada shirye-shiryensa kan harkokin Musulunci.
Saboda haka sai ya ce gwamnati da Hukumar Hajji ta kasa na bukatar malamai da gidajen wasta labarai irin Gidan Talabijin na Manara masu yada shirye-shirye a kan Musulunci.
Daga bisani sai ya yi kira ga hukumomin Saudiyya su janye harajin da suka sanya wa alhazan da suke son komawa aikin Hajji a shekara mai zuwa.
Ya bayyana cewa idan har hukumomin Saudiyya suka rage harajin da suka sanya babu shakka alhazan Najeriya za su ji dadi kuma za su samu sauki.
Ya shawarci hukumomin kasar Saudiyya su rika saukaka wa alhazan Najeriya ka’idojin shiga kasar ta yadda jama’a za su samu saukin gudanar da ibadojinsu kamar yadda ya kamata.