Ya nemi Gwamnatin Jigawa ta gina Cibiyar Nazarin Alkur’ani
Mai ba Gwamnan Jihar Jigawa shawara a kan harkokin addini Alhaji Isa Duniya-Ba-Hutu ya nemi gwamnatin jihar ta samar da Cibiyar Nazarin Alkur’ani a jihar.Alhaji Isa Duniya-Ba-Hutu wanda shi ne tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na jihar ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wurin bude gasar musabaka ta jihar, inda ya ce samar […]
SONY DSC

Mai ba Gwamnan Jihar Jigawa shawara a kan harkokin addini Alhaji Isa Duniya-Ba-Hutu ya nemi gwamnatin jihar ta samar da Cibiyar Nazarin Alkur’ani a jihar.
Alhaji Isa Duniya-Ba-Hutu wanda shi ne tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na jihar ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wurin bude gasar musabaka ta jihar, inda ya ce samar da cibiyar zai taimaka wajen saukar baki a yayin gudanar da gasar a jihar.
Ya shawarci mahaddata Alkur’ani da malamai su rika yi wa shugabanni addu’ar alheri, yayin da ya shawarci shugabanni su guji yi wa ni’imomin Allah rikon sakainar kashi.
A jawabin Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi ya ce shigowar wannan gwamnatin an samu ci gaba ta fuskar addini, inda a yanzu harkokin addini ke kara habaka.
Sarkin ya ce an samu raguwar shaye-shaye a tsakanin matasan jihar sakamakon gudunmawar da suke samu ta fuskar nazarin Alkur’ani wadda musabakar ke karfafa ta.
Ya shawarci alkalan masabakar su zama masu adalci a lokacin gudanar da musabaka ta jihar, wadda ita ce za ta karbi bakuncin mahaddata da za su halarci gasar musabaka ta kasa a bana.
Shugaban majalisar jihar Alhaji Adamu Atamos Sarawa wanda ya wakilci Gwamna Sule Lamido y ace gwamnatin jihar a shirye take domin taimaka wa masu gudanar da gasar, kuma kofarta a bude take don taimaka wa addinin Allah a koyaushe.
Ya ce gwamnatin jihar za ta yi tsayin daka a kokarinta na taimaka wa wadanda suka zamo zakaru a gasar ta kasa da za a gudanar a jihar a bana. Sai ya hori wakilan jihar su zama masu da’a ga malamansu a lokacin gudanar da masabakar, su kuma alkalan su zama masu adalci su guji tauye wa dalibai hakkinsu a lokacin gasar musabakar.