Ya nemi hadin kan mahauta domin samun zaman lafiya
Sarkin fawan Benin, Shehu Usman Abdullahi ya nemi jama’arsa masu sana’ar fawa su manta da bambance-bambance da ke tsakaninsu da kuma na sauran ’yan kasuwa da mazauna garin Benin domin a samu dorewar zaman lafiya da kuma ci gaban sana’ar tasu.Sarki Shehu, wanda ya bayyana bukatar hakan a wata hirarsu da ja Aminiya, yana bayyana […]

Sarkin fawan Benin, Shehu Usman Abdullahi ya nemi jama’arsa masu sana’ar fawa su manta da bambance-bambance da ke tsakaninsu da kuma na sauran ’yan kasuwa da mazauna garin Benin domin a samu dorewar zaman lafiya da kuma ci gaban sana’ar tasu.
Sarki Shehu, wanda ya bayyana bukatar hakan a wata hirarsu da ja Aminiya, yana bayyana takaicinsa ne kan wata takaddama da ta tasar ma kawo baraka tsakanin mahauta na Hausawan da junansu a kan wani batun da wasu ke goyon bayansa da bangaren da ba sa goyon bayan shirin.
Ya ce, “Muna godiya ga Allah da Ya kawo daidaituwar lamarin, sannan muna yaba wa Sarkin Eyaen, Dokta Osazuwa A. Iduriase ya sa baki ya sulhunta tsakanin bangarorin biyu. Wajibi ne mu yaba wa Dokta Osazuwa namijin kokarinsa da ya yi tare da kaunar da yake yi wa ’yan Arewa ya sasanta wannan rikicin cikin hikima da ruwan sanyi. Ba don hakan da ya yi ba da rikicin zai kai ga bata mana zama a garin Benin.
“Ina kira ga daukacin mahautan Hausawa na garin Benin da su gane cewa neman arziki ya tara mu a garin, don haka mu rungumi juna a matsayin ’yan uwa, mu bar nuna gaba tsakanin juna, kuma mu rike sana’armu tsakani da Allah”.