Ya nemi masu hali su kafa kamfanoni don rage rashin aikin yi
Shugaban kungiyar Motocin Sufuri ta kasa (NARTO) reshen Jihar Nasarawa, Alhaji Maiwada Sidi ya bukaci al’ummar Najeriya su rika bude kamfanoni da masana’antu domin samar wa matasa aikin yi ta yadda za a rage dogara da aikin gwamnati. Alhaji Maiwada Sidi ya bayyana haka ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa da […]
Shugaban kungiyar Motocin Sufuri ta kasa (NARTO) reshen Jihar Nasarawa, Alhaji Maiwada Sidi ya bukaci al’ummar Najeriya su rika bude kamfanoni da masana’antu domin samar wa matasa aikin yi ta yadda za a rage dogara da aikin gwamnati. Alhaji Maiwada Sidi ya bayyana haka ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Keffi inda ya ce hatta kungiyar NARTO ya kawo ta Jihar Nasarawa ne a kokarinsa na rage yawan masu zaman kashe wando, “Saboda a kullum tunanina shi ne yadda zan yi in samar wa matasa aikin yi ba sai sun dogara da gwamnati ba, kuma ni babu harkar da na kware kamar wadanda suka shafi sufuri, kasancewata tsohon direba da na yi kimanin shekara 25 ina tuki,” inji shi.
Ya ce ya dauko kungiyar NARTO ne daga Zariya a wajen Alhaji Umaru 7up inda suka shirya suka bi dokokin kungiya da ke cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, sannan ya kawo ta Keffi a ranar 23 Fabrairun shekarar 2013. Shugaban ya ce ganin yadda ya samu nasarar kawo kungiyar NARTO, ya sake tunani don bude wani kamfani mai suna Maiwada Sidi Motors Transport LTD domin samar wa matasa aikin yi ta hanyar ba su hayar motoci da babura da wasu kayayyakin masarufi don ceto su daga mawuyacin halin rayuwa.