Ya nemi ’yan Arewa su mara wa PDP baya a zaɓen Gwamnan Edo

Duk mai hankali ya tabbatar siyasa da gaba ba ta da alfanu, domin gaba ba ta kawo ci-gaba.

Ya nemi ’yan Arewa su mara wa PDP baya a zaɓen Gwamnan Edo

Wani jigo a jam’iyyar PDP kuma jagorar ’yan Arewa a Jihar Edo, Alhaji Sahabi Aliyu Umar (JP), ya yi kira ga ’yan Arewa mazauna jihar su tabbatar sun ba jam’iyyar PDP mai ci a jihar goyon baya a zaɓen da za a yi ’yan watanni kaɗan masu zuwa.

Alhaji Sahabi Umar ya yi kiran ne a hirarsa da Aminiya a inda ya nuna gamsuwa da shirye-shiryen da jam’iyyar ke yi don ganin ta sake lashe zaɓen jihar.

Ya ja hankalin ’yan Arewa su haɗa kansu su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya saboda samun nasara, sannan ya yi gargaɗin da su guji yin siyasar gaba.

“Duk mai hankali ya tabbatar siyasa da gaba ba ta da alfanu, domin gaba ba ta kawo ci-gaba.

“Matuƙar muna son samun ribar mulkin dimokuraɗiyya sai mun jefar da nuna gaba a tsakaninmu mun rungumi hanyar samun ci-gaba da zaman lafiya,” in ji shi.

Alhaji Sahabi ya kuma ƙara gargadi kan a guji tashin hankali a lokacin zaɓen yana mai kira ga jama’a su natsu a ranar zaɓe, su je su kaɗa ƙuri’unsu ba tare da tashin hankali ko fitina ba.

A ranar Asabar, 21 ga watan Satumbar bana ne dai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC za ta gudanar da zaɓen gwamna a Jihar Edo.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja