Ya nemi ’yan siyasa su rika taimaka wa wadanda suka zabe su
dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Keffi da Karu fa Kokona a Jihar Nasarawa, Mista Jonathan Gaza Gbefwi ya shawarci ’yan siyasa su kasance masu tsoron Allah da zama masu zukatan taimaka wa na kasa da su da abubuwan da suke bukata a yankunansu.Mista Jonathan Gaza ya bayyana haka ne a fadar Sarkin Keffi wajen wani […]
dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Keffi da Karu fa Kokona a Jihar Nasarawa, Mista Jonathan Gaza Gbefwi ya shawarci ’yan siyasa su kasance masu tsoron Allah da zama masu zukatan taimaka wa na kasa da su da abubuwan da suke bukata a yankunansu.
Mista Jonathan Gaza ya bayyana haka ne a fadar Sarkin Keffi wajen wani taron tallafi da ya shirya inda ya ba mata kayakin sana’o’i kamar kekunan dinki, injunan markade da atamfofi da yaduna da kudi ga al’ummar mazabarsa.
A zantawarsa da Aminiya Mista Jonathan Gaza ya ce zai so jama’a musamman ’yan siyasa su san cewa albarkar juna suke ci su da talakawa. Ya ce ba don talakawa ba babu dan siyasar da zai kai inda yake, “Kuma in muna son mu sake neman wani matsayi nan gaba to yanzu ne ya dace mu taimaka wa talakawa mu daraja su, in muka yi haka za su yi alfahari da mu,” inji shi.
Sai dai ya ce kada jama’a su rika tunanin sun zabi wani ne don ya kasance mai raba musu kudi a koyaushe, domin irin wannan halin ne ya sa wasu ’yan siyasa marasa tunani ke yi wa jama’a kallon kaji da an watsa musu tsaba za a kama su.
Jonathan Gaza ya ce, duk dan siyayar da ya butulce wa jama’arsa siyasarsa ba za ta yi karko ba, domin Hausawa na cewa kowa ya ci ladan kuturu sai ya yi masa aski. “Da wannan dalili ne ya sa na yi tunanin taimaka wa jama’ata don nuna musu cewa na san darajarsu. Su ma ina bukatar su fahimci kudirina na alheri a gare su, haka ina kira ga ’yan uwana ’yan siyasa da ke rike da kujeran mulki su tashi haikan domin taimaka wa jama’arsu domin gaba ta fi baya yawa.