Ya nuna takaicin halin da wasu al’umma suke ciki

Daraktan agaji na kungiyar Munazzamatu Fityanul Islam ta Najeriya, Alhaji Kabiru Ahmad Gusau ya nuna takaicinsa kan yadda ake sako-sako da neman ilimi a kasar nan.Domin magance wannan matsala ce, daraktan ya ce nan ba da jimawa ba ne kungiyar tasu ta agaji za ta kafa jami’ar Musulunci a Kano. Ya bayyana haka ne a […]

Ya nuna takaicin halin da wasu al’umma suke ciki
Ya nuna takaicin halin da wasu al’umma suke ciki

Daraktan agaji na kungiyar Munazzamatu Fityanul Islam ta Najeriya, Alhaji Kabiru Ahmad Gusau ya nuna takaicinsa kan yadda ake sako-sako da neman ilimi a kasar nan.
Domin magance wannan matsala ce, daraktan ya ce nan ba da jimawa ba ne kungiyar tasu ta agaji za ta kafa jami’ar Musulunci a Kano. Ya bayyana haka ne a yayin zantawarsa da Aminiya a garin Kalaba, lokacin da shugabannin kungiyar suka kai ziyara Jihar Kurosriba. Shugabannin kungiyar karkashin jagorancin Alhaji Ahmad Gusau da tawagarsa wadda ta kunshi Alhaji Sharif Bala danlawan, sakataren tsare-tsare na kasa da kuma sakataren mulki, Malam Ibrahim Abubakar na ziyarar jihohin yankin Kudu maso kudu ne halin yanzu. Domin su gane wa idonsu yadda sauran rassan kungiyar na yankin suke ciki, da ma al’ummar Musulmi da ke zaune a yankin.
Babban-Daraktan ya ci gaba da cewa: “Alhamdu lillahi, ita wannan kungiya tun farkon soma ta, ta fara ne da gina makarantun matakin firamare da na sakandare, sannan kuma tun daga wannan lokacin kowane reshe na jiha na kungiyar yana kokarin shi ma ya gina makarantu na firamare da na sakandare a yankinsa. Yanzun ma muna nan muna kokarin gina jami’a ta Musulunci, muna ma da filin yanzu haka yana na a hedkwatar kungiyar da ke  Kano, Jihar Kano, wanda wadannan makarantu da suke a jihohi za su rika zuwa wannan  jami’a domin kara karatunsu, su kuma samu satifiket na Musulunci. “Inji shi.
Da ya juya kan sauran kungiyoyi masu yi wa Musulunci aiki a Najeriya domin ci gabansa dana Musulmi, ya kara da cewa: “Yan uwa Musulmi mazauna sassan kudancin kasar nan na bukatar a rika ziyartarsu domin karfafa dankon zumunci da kuma ganin halin da suke ciki, musamman irin yadda akan samu ’yan asalin wadannan yankuna suna karbar Musulunci kuma suke bukatar kulawa ta musamman, ta hanayar karantar da su da kuma taimaka masu. karancin wannan yana kawo ci baya, musamman ga masu shigowa Musulunci.”
Alhaji Kabiruya ce yana ganin irin yadda ake sako-sako da wasu al’amuran tallafa wa wadanda suka shiga Musulunci a kudanci, suka rabu da danginsu sanadin haka, ba su samu wata kulawa ba daga Musulmin da ke zaune a wadannan yankuna na haifar da cikas. Ya ce mafita kawai ita ce: “Dukkannin wani mai kungiya ta addinin Musulunci, ya yi kokari ya rika kai ziyara wuraren da Musulmi ba su da yawa, domin a rika fadakar da su, a rika nuna masu wasu hanyoyin da za su rika  tallafa wa wadanda suke zaune a yankunan, suka shiga Musulunci.”
Ya ce halin da ake ciki kungiyar ta fara shirye-shiryen bikin cika shekara 53 da kafa ta, inda nan gaba kadan idan an kammala shirye-shiryen bikin, za a sanar da lokacin da za a yi shi.