Ya rasa ransa a yayin da yake waya da wata mata
Wani mai sana’ar achaba a garin Kubwa na yankin Birnin Tarayya Abuja mai suna Habila Ibrahim ya rasa ransa a daidai lokacin da yake yin waya da wata. Lamarin wanda ya faru a ranar Talatar da ta gabata da misalin karfe 7 na dare, kamar yadda wani dan uwan marigayin mai suna Sahabi Ibrahim ya […]

Wani mai sana’ar achaba a garin Kubwa na yankin Birnin Tarayya Abuja mai suna Habila Ibrahim ya rasa ransa a daidai lokacin da yake yin waya da wata. Lamarin wanda ya faru a ranar Talatar da ta gabata da misalin karfe 7 na dare, kamar yadda wani dan uwan marigayin mai suna Sahabi Ibrahim ya bayyana wa Amniya, ya ce da farko wansa mai shekara 30 wanda dan asalin garin Tsiga ne da ke karamar hukumar Bakori ta Jihar Katsina da ke da mata daya da kuma ’ya’ya biyu, ya fara yin wayan ne tun daga dakinsa da wata mai suna maman Blessing, kamar yadda aka gano daga bisani, inji shi, amma sai wayar ta katse bayan karewar kudi.
Ya ce marigayin ya fito waje a unguwarsu da ke farm shelter a yankn Biyaji na garin Kubwa inda ya sayi kati waya, sai dai bayan ya fara wayar na dan lokaci sai ya yanke jiki ya fadi a gaban mutane.
Ya ce an dauke shi a kan babur inda aka sa shi a tsakiya kuma tun daga kan hanya aka kula da cewa ya sake jikinsa sannan ya kara nauyi.
“Bayan mun isa asibti sai aka tabbatar mana da cewa ya rasu. ’Yan acaba da dama sun yi dafifi a asibitin Kubwa a shekaranjiya Laraba don amsar gawar marigayin wadda za a kai gida.
Da Aminiya ta tambayi dan uwan ko mai ya sa ’yan Achaba a wasu lokuta ke da dabi’ar kai gawan mamatansu gida, sai dan uwan ya ce, “ Yawancinmu da ka gani a nan maguzawa ne ko kiristoci, a dalilin haka ne mu ke kai gawa gida don yi mata sutura tare da biki. Babban jami’in ’yan sanda na garin Kubwa wato DPO, CSO Ayobami Surajudeen ya ce ba a sanar da su labarin ba.