Ya rasa ransa wajen ceto matan da ambaliya ta ja a Nasarawa
Wani magidanci mai suna Muhammadu Tindi da ke Unguwar Kilema a Karamar Hukumar Lafiya a Jihar Nasarawa ya rasa ransa bayan da ya shiga ruwan da ke ambaliya don nufin ceton wadansu mata da ruwa ya ja su. Da yake yi wakilinmu bayanin yadda lamarin ya faru, wani wanda abin ya faru a idonsa mai […]
Marigayi Muhammadu Tindi
Wani magidanci mai suna Muhammadu Tindi da ke Unguwar Kilema a Karamar Hukumar Lafiya a Jihar Nasarawa ya rasa ransa bayan da ya shiga ruwan da ke ambaliya don nufin ceton wadansu mata da ruwa ya ja su.
Da yake yi wakilinmu bayanin yadda lamarin ya faru, wani wanda abin ya faru a idonsa mai suna Umar Muhammadu Mai’unguwa ya ce, “Marigayin wanda sannane da yanke sana’ar wankin mota a bakin rafin Amba tsawon shekaru, ranar da ruwan ya yi ambaliya, sai matasa suka rika rike hannun masu sauri wadanda ba za su iya jiran ruwan ya ragu ba. Ruwan ya shafe kan gadar da ke wurin, kuma bayan awanni ruwan bai janye ba, sai matasa suka rika kabar Naira hamsin suna kama hannun mutane suna hayewa da su daga wannan gabar zuwa waccan gabar.”
Mai’unguwa ya kara da cewa, “Ana cikin haka sai wadansu mata masu kasuwanci ’yan kabilar Ibo suka ce ba su da ko sisi, sai suka shiga ruwan da kansu, kuma suna kaiwa tsakiyar gada, sai ruwa ya ja su, suka fada rafin, ganin haka ne shi Muhammadu Tindi ya fada ruwa don ceto su, amma sai igiyar ruwa ta nutsar da shi da wacce ya je ya ceto, shi ya rasu daya daga cikin matan ruwa ya tafi ita sannan an samu ceto daya daga cikinsu a galabaice.”
Malam Umar Mai’unguwa ya kara da cewa, sai da gari ya waye ruwan ya janye sannan aka samu tsamo gawar Muhammadu Tindi, kuma tuni aka yi jama’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.