Ya rasa ransa wajen gwajin maganin bindiga
Wani saurayi dan shekara 25, mai suna Osamame Osekhere ya rasa ransa a wajen gwajin maganin bindiga da suka yi shi da abokinsa a kasuwar Oba da ke Birnin BininAminiya ta samu labarin cewa, amtashin ya rasa ransa ne a lokacin da yake gwada asirin bindiga da ake yi wa lakabi da “Inshorar Afirka – […]
Wani saurayi dan shekara 25, mai suna Osamame Osekhere ya rasa ransa a wajen gwajin maganin bindiga da suka yi shi da abokinsa a kasuwar Oba da ke Birnin Binin
Aminiya ta samu labarin cewa, amtashin ya rasa ransa ne a lokacin da yake gwada asirin bindiga da ake yi wa lakabi da “Inshorar Afirka – African insurance,” tare da abokinsa, wanda ba a bayyana sunansa ba.
Harbin da aka yi w matashin ya haifar da rudani a kasuwar, inda matasa suka fara zanga-zangar kin nuna amincewa da kisan. Wannan al’amari dai ya sanya mafi yawan ‘’yan kasuwar sun kulle kantunansu, sun fice daga harabar wurin.
Wani da al’amarin ya faru a gabansa, ya bayyana cewa, shi Isuekhuere ne ya gayyaci daya daga cikina bokansa da ya harbe shi a matsayin gwajin sabuwar layar maganin harsahin bindiga da ya samu; kuma said a marigayin ya fara gwada harbin a kan abokinsa, amma harsashin bai huda shi ba.
Sai dais hi ma a lokacin da abokin nasa ya harbe shi a irji, harsashin bindigar bai huda shi ba, amma da ya sauka akan jikinsa, sai ya ratsa shi, al’amarin da ya zama sanadiyyar halakarsa. Abokan mamacin sun kona dakin abokinsu da ya harbi wannan saurayi har ya mutu.
Da aka tuntubi jami’in ’yan sanda, mai magana da yawunsu a Jihar Binin, Uwoh Noble, ya ce bai samu bayani kan aukuwar lamarin ba.