Ya rataye kansa saboda ya kasa biyan sadaki

Al’ummar garin Gante-Tudu da ke Ka’oje a karamar Hukumar Bagudo a Jihar Kebbi sun ga abin al’ajibi a ranar Asabar da ta gabata, yayin da wani matashi mai shekara 30 mai suna Abubakar Ahmed ya kashe kansa saboda bai samu rancen Naira dubu 40 don biyan sadakin kara aure ba.Abubakar Ahmed ya kashe kansa ne […]

Ya rataye kansa saboda ya kasa biyan sadaki
Ya rataye kansa saboda ya kasa biyan sadaki

Al’ummar garin Gante-Tudu da ke Ka’oje a karamar Hukumar Bagudo a Jihar Kebbi sun ga abin al’ajibi a ranar Asabar da ta gabata, yayin da wani matashi mai shekara 30 mai suna Abubakar Ahmed ya kashe kansa saboda bai samu rancen Naira dubu 40 don biyan sadakin kara aure ba.
Abubakar Ahmed ya kashe kansa ne ta hanyar rataye kansa da igiyar da ake daure rakuma a gindin wata bishiya da ke kan hanyar shiga kauyen na Gante-Tudu a daidai ranar da ta kamata a daura masa auren amma sanadin rashin kudin sadakin sai aka daga auren zuwa yau 7/2/2014.
Shi dai marigayin ana hasahen ya yanke shawarar kashe kansa ne bayan ya je wurin wani abokinsa neman bashin kudin a wani kauye da ake kira Buya bai samu ba.
Marigayin ya shafe shekara biyu yana neman budurwar da yake so ya aura, kuma lamarin ya faru ne a daidai lokacin da uwargidansa ta koma gidansu domin haihuwa.
Wata majiya daga gidansu ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa marigayin ba ya da wata rashin lafiya ko kuma tabin hankali.
Shugaban karamar Hukumar Bagudo Alhaji Bello Abdullahi Ka’oje ya tabbatar da faruwar lamarin.
Lokacin da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi Sufurtanda Muhammad ya ce yana Abuja wajen wani aiki.