Ya raunata kansa ya ce an yi masa fashi don kada ya saya wa budurwarsa mota
Wani dan kasar China da ake kiransa da sunan mahifinsa wato Tang, ya dauki alkawarin da ba zai iya cikawa yayin bai da isassun kudi amma ya yi wa budurwarsa alkawarin saya mata mota mai tsada. Tang ya dauki budurwarsa Yang da wadansu ’yan uwanta biyu zuwa wajen dillalin motoci inda ya ce zai biya […]
Wani dan kasar China da ake kiransa da sunan mahifinsa wato Tang, ya dauki alkawarin da ba zai iya cikawa yayin bai da isassun kudi amma ya yi wa budurwarsa alkawarin saya mata mota mai tsada.
Tang ya dauki budurwarsa Yang da wadansu ’yan uwanta biyu zuwa wajen dillalin motoci inda ya ce zai biya kudin China Yuan dubu 700, (kimanin Naira miliyan 3 6, da dubu 849 da 331 da kwabo 21) don sayan wa budurwar motar alfarma alkawarin da ya yi mata ranar Alhamis 16 ga Agustan 2018.
Tang ya ce, ya biya kudin China Yuan dubu 10, a matsayin somin-tabi, amma lokaci da suka isa wurin masu sayar da motoci sai Tang ya ce wa budurwar su jira shi zai je ya dauko kudi don biyan kudin motar. Kuma maimakon ya tafi kamar yadda fada, sai ya shiga wani kantin sayar da kayyaki ya sayo wuka a kan Yuan 15, saboda ya san ba ya da kudin motar sai ya boye a bayan wasu motoci a kantin ya yanki hannunsa.
Nan take ya kira budurwarsa a waya yana fada mata cewa, an yi masa fashi da makami an kuma sace masa Yuan dubu 750.
Sai dai burin Tang bai cika ba, saboda bayan ya sanar wa budurwar abin da aka yi masa, sai budurwar ta kira ’yan sanda nan take inda sauran ’yan uwanta suka wuce da Tang asibiti don yi masa jinya.
A yayin da ’yan sanda suke binciken Tang a kan lamarin ne sai ya fada musu gaskiyar abin da ya faru cewa, da farko ya yi wa budurwarsa karyar cewa, shi attajiri ne sosai alhali akasin haka ne.
’Yan sanda sun tsare shi har na kwana goma tare da cin tararsa na Yuan 500.