Ya rayu bayan awa 10 da fashewar kwalekwalensa a teku
Wani mutum ya tsallake rijiya da baya bayan kwashe tsawon awa 10 igiyar ruwa na fizgar sa a kan teku bayan fashewar kwalekwalensa. Mutumin, wanda aka ceto shi a galabaice, ya shiga tsaka mai wuya ne bayan ya shiga tekun a cikin wani kwalekwale da ake buga wa iska, a kusa da County Louth na […]
Wani mutum ya tsallake rijiya da baya bayan kwashe tsawon awa 10 igiyar ruwa na fizgar sa a kan teku bayan fashewar kwalekwalensa.
Mutumin, wanda aka ceto shi a galabaice, ya shiga tsaka mai wuya ne bayan ya shiga tekun a cikin wani kwalekwale da ake buga wa iska, a kusa da County Louth na sakar Ireland.
Yana tsaka da yawo a kan tekun ne kwalekwalen ya fashe, inda daga nan ya shafe awa 10 igiyar ruwa na yawo da shi, yana neman ceto zuwa gabar teku, amma bai samu dauki ba.
Da misalin karfe 10 saura kwata na dare, agogon kasar Ireland, ’yan sanda suka sanar da cewa masu gadin bakin teku sun ji ihu a tekun, kafin aka tura masu ceto suka gano shi.
Kafar watsa labarai RTÉ ta kasar Irelan ta ce a ranar Litinin, 26 ne ga Yuli, 2021 mutumin mai shekarau 40 da wani abu, dan asalin yankin Newry a Arewacin kasar, ya yi kasassabar a Tekun.
A halin yanzu dai an garzaya da mutumin zuwa asibitin Beaumont da ke birnin Dublin.
‘Kayan wasa ne’
Cibiyar kula da ayyukan ceto a Dublin, Kilkeel, ta ce wani helikwaftan masu aikin ceto da kuma wani karamin jirgin ruwa ne suka yi aikin ceto shi.
Ta kara da cewa masu gadin gabar teku sun shaida mata cewa rigar hana nutsewa a ruwa da yake sanye da ita ce ta taimaka masa ya dade a kan tekun.
Shugaban ayyuka na hukumar kula da teku na kasar, Gerard O’Flynn, ya nbayyana cewa mutumin ya tsallake siradi ne bayan ya yi gangancin shiga teku a kan “abin wasa na kasada”.
Ya yi kira ga jama’a da su guji amfani da kwalekwalen da ake buga wa iska a cikin rafi ballantana teku.
Su “kayan wasan baya ne na nishadi kuma iya inda ya kamata a yi amfai da su ke nan,” inji Mista O’Flynn.