Ya rayu bayan zuma ta harbe shi fiye da sau 500

Wani mutum ya rayu bayan da kudan zuma ya harbe shi sau 500 zuwa 1000, kamar yadda shafin intanet na Yahoo News ya ruwaito.  Al’amarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata, a Jihar Arizona ta kasar Amurka, kamar yadda mahukunta suka bayyana.Mutumin wanda ba a kai ga bayyana sunansa ba, yana karbar […]

Ya rayu bayan zuma ta harbe shi fiye da sau 500
Ya rayu bayan zuma ta harbe shi fiye da sau 500

Wani mutum ya rayu bayan da kudan zuma ya harbe shi sau 500 zuwa 1000, kamar yadda shafin intanet na Yahoo News ya ruwaito. 

Al’amarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata, a Jihar Arizona ta kasar Amurka, kamar yadda mahukunta suka bayyana.
Mutumin wanda ba a kai ga bayyana sunansa ba, yana karbar kulawa daga wani asibiti bayan kudan zuman sun dabaibaye a wani wuri da ake kiwonsu.
Wani jami’in asibitin da mutumin yake karbar kulawa, ya ce abin ya yi kama da irin abin da ake gani a fina-finan talabijin, ya ce, “abin, abin al’ajabi ne.”
An dai ruwaito cewa al’amarin ya faru ne lokacin da mutumin ya shiga wani wurin da ake kiwon kudan zuman, inda nan take suka tasamme, kafin daga bisani ya samu taimako daga wasu mutane da suka zo wuce wa.
Har ila yau, mahukuntan yankin sun shawarci iyayen yara da su dinga barin ’ya’yansu a cikin gida saboda kauce wa sake faruwar lamarin. Masu motoci kuma an bukaci da su dinga barin tagogin motocinsu a rufe.