Ya rayu shekara 53 da kudin karfe a cikin hancinsa
Wani mutum mai shekara 59 a birnin Zelenograd da ke kasar Rasha wanda ya yi fama da matsalar numfashi sama da shekara 50, an gano ashe ya zura wani kudin karfe ne a cikin hancinsa ya manta da shi tun yana yaro kuma ba a gano matsalar ba sai daga bayan nan da likitoci suka […]
Wani mutum mai shekara 59 a birnin Zelenograd da ke kasar Rasha wanda ya yi fama da matsalar numfashi sama da shekara 50, an gano ashe ya zura wani kudin karfe ne a cikin hancinsa ya manta da shi tun yana yaro kuma ba a gano matsalar ba sai daga bayan nan da likitoci suka gudanar da bincike.
Likitocin da suka duba mara lafiyar a asibitin Konchalobsky City Clinical a birnin Zelenograd sun fitar da rahoton abin mamakin da ya suka gano daga mutumin da aka kai musu asibitin kan rashin yin numfashi ta kofar hancinsa ta hannun dama a tsawon watanni.
- ‘Yadda ’yan bindiga suke tilasta mana kwana a jamhuriyar Nijar kullum da yamma’
- Nakasassu sun tare ofishin gwamna kan kin daukar su aiki
Bayan daukar hoton cikin hanci da aka yi da na’ura ne aka gano cewa kafar shakar numfashinsa ta toshe da wani abu da aka zura a ciki mai kama da dutse.
Sannan an gano cewa, toshe kofar shakar numfashi na daga ciki dalilin da ya sa baya iya yin numfashi, sai dai toshewar ba ta yi sanadin da zai sa ya gaza shakar numfashin gaba daya ba.
Wannan kudin karfe da ya zura tun yana yaro shi ne babban matsalar da ta yi ta karuwa tun yana numfashi kadan-kadan har ta kai ga ba ya iyawa gaba daya sai da ya nemi taimakon likita.
Mara lafiyar bai taba sanar da likitoci cewa ya taba zura wani abu a cikin hancinsa ba, sannan ya ce ba zai iya tuna dalilin da ya sa zura sulallan kudin a cikin hancinsa ba.
Bayan fitar da hoton da aka yi na cikin hancin sai aka gano kudi ne na karfe a cikin kofar numfashinsa, daga nan ya fara tuna lokacin da yake wasa da kwabbai yana dan kimanin shekara shida inda ya zura daya daga cikinsu a cikin hancinsa.
Saboda mahaifiyarsa wadda aka sakaya sunanta tana da fada, sai ya ji tsoron fada mata abin da ya faru bayan ya zura kudin a cikin hancin.
A haka ya ci gaba da rayuwa da kudin a cikin hancinsa bayan wani lokaci sai kawai ya manta da abin da ya zura a cikin hancin.
Likitoci sun yi matukar razana bayan jin bayanin da ya yi kan dalilin barin kudin a cikin hancinsa. Bayan tiyatar ciro kudin da aka yi wadda ta kai tsawao awa daya da rabi ana yi, likitocin sun amince da bayanin da mara lafiyar ya yi.
Sakamakon dadewar da kudin ya yi a cikin hancin har ya samu gurbi a cikin hancin.
A lokacin da ake kokarin ciro kudin daga cikin hancin, likitoci sun yi kokari sauya gurbin shakar numfashin inda a lokacin ya fi samun cikakkiyar iskar da zai iya shaka.
Wani kwararren likita mai suna Elena Nepryakhina ya bayyana wa kafar labarai ta Moscow Press Agency cewa sakamakon toshewar kafar shakar numfashin sai da ta kai ga mutumin ya yi rashin lafiya, amma nan gaba kadan zai samu cikakkiyar lafiya.
Likitocin sun ce, mara lafiyar ya yi nasara sakamakon maido masa da hanyoyin shakar numfashinsa da suka toshe na tsawon shekaru.
A cewar likitocin marar lafiyar ka iya samun wasu matsaloli sakamakon barin wani karfe a jikinsa na tsawon lokaci, amma sai dai kawai matsalar numfashi ya fuskanta.