Ya rayu shekara 9 da guntun gilashi a cikin hantarsa

AAmma likitoci sun cire gilashin ba tare da wata matsala ba.

Ya rayu shekara 9 da guntun gilashi a cikin hantarsa

Wani ɗan ƙasar Rasha da ya riƙa fama da ciwo a cikinsa da ƙarƙashin haƙarƙarinsa a tsawon shekara tara da suka wuce, ya yi matuƙar kaɗuwa da aka gano cewa yana ɗauke da wani guntun gilashi mai tsawon santimita 9 a cikin hantarsa.

Mutumin mai shekara 53 da ba a bayyana sunansa ba, ya shaidawa likitocin Asibitin Kirox Regional Clinical Hospital da ke ƙasar Rasha cewa ya daɗe yana fama da matsanacin ciwo da rashin jin daɗi a ɓangaren dama na jikinsa da ƙarƙashin haƙarƙarinsa, amma bai damu a duba shi ba.

Bayan da ya yanke shawarar neman taimakon likita a kan matsalarsa, an yi masa hoton inda yake masa ciwo, inda aka gano wani abu mai kaifi a maƙale a gefen dama na hantarsa.

Lokacin da likitoci suka tambaye shi yadda abin ya shiga cikinsa, majinyacin ya gaya musu cewa ba ya da masaniya, saboda ba ya da tarihin raunin, kuma ba zai iya tuna wani abu mai kaifi ya shiga jikinsa ba.

Bayan yi masa tiyata, likitocin sun cire gilashin mai tsawon santimita 9 daga jikin hantarsa.

“Mun yi mamaki lokacin da muka ga guntun gilashin mai girma milimita 88ɗ15ɗ7 tare da kaifi bayan duba na’urar madubin bincike,” in ji ɗaya daga cikin likitocin.

“A yayin tiyatar, an gano cewa akwai baƙon abu da wasu halittun suka lulluɓe.

“Wannan shi ne yadda jiki ke amsawa ga kutsawar wani baƙon abu.

“Yana haddasa kumburi a wajen da zai iya yin illa, kuma ana iya samun wasu halittu da suke lulluɓe baƙon abu, wanda ke bambanta su da halittu masu kare lafiyar jikin.

Mutumin mai shekara 53 ya yi sa’a sosai don ya rayu tare da baƙon abu da ke cikin hantarsa na sama da shekara 9, saboda yana iya haifar da kumburin cikin sauƙi da tsananin ciwo, wanda zai buƙaci tiyata ta gaggawa.

“Duk da haka, aikin tiyatar da aka yi don cire gilashin ya kasance mai haɗari sosai saboda wadatar jini da hanta ke ɗauke da shi, amma likitocin sun cire gilashin ba tare da wata matsala ba.

An yi ta yada hotunan gilashin a shafukan sada zumunta na Rasha, lamarin da ya sa mutane ke mamakin yadda mutumin ya sha fama da raɗaɗin ciwon da ya yi kusan shekara goma kafin daga baya ya yanke shawarar ganin likita a kai.

 

Abba ya yi tafiya yayin da rikici ya dabaibaye NNPP a Kano

Kotu ta hana EFCC kama tsohon minista kan taƙaddamar fili

Isra’ila ta ɗaiɗaita yara sama da 400,000 a Lebanon — UNICEF

Ba zan ce uffan kan rikicin NNPP a Kano ba — Kwankwaso