Ya sa an yanke kafafunsa don samun kuɗin inshora

Tsarin da ba a shirya ba aka yi ne, ban taba ganin wani abu mai kama da haka ba.

Ya sa an yanke kafafunsa don samun kuɗin inshora

Ofishin shugaban ’yan sandan (Sheriff) da ke kula da waɗanda ake tura su gidan yari na Gundumar Howell a kasar Amurka, ya fara bincike a kan wani lamari mafi ban mamaki a tarihinsa.

A watan Nuwamban bara ce, wani mai shekara 60 daga ƙauyen Willow Springs ya rasa kafafunsa biyu bayan da aka zarge shi da yin haɗari da motar yankar ciyawa.

Shi dai wannan haɗari na da alaƙa da yadda aka saba maƙala wa masu tuƙa taraktoci, kuma mutumin ya yi ikirarin cewa an yanke kafafun biyu ne da gangan.

Sai dai duk da haka, akwai tasgaro a cikin labarin mutumin.

Da farko dai, a zahiri ya rasa kafafunsa, kamar yadda babu inda aka same su, wanda ke da ban mamaki ga irin wannan haɗarin motar.

Sannan akwai gaskiyar cewa raunukan mutumin sun yi tsafta ganin irin wannan haɗarin mota ne ya haddasa shi.

Kuma a karshe, mutumin ya kasance sanannen gurgu, wanda ya haifar da tambayoyi game da yadda ya yi haɗari da motar gyaran ciyawa na tarakta.

Torey Thompson, wani Laftanar a Ofishin Sheriff na Gundumar Howell County, ya shaida wa kafar labarai ta Springfield News Reader cewa: “Idan aka yi la’akari da cewa ya yi haɗarin ne da motar da yake ciki, raunin ya yi muni zai zama yana zubar da jini, wanda zai zama tashin hankali.

“Na taba ganin irin wadannan hadurra a baya. Wanda nasa ba haka yake ba.”

Jami’ai da ma’aikatan lafiya da aka kira wurin da haɗarin ya auku, su ma sun nuna matuƙar mamaki a kan dungulmin kafafunsa da wanda ya sanya su nan da nan bayan haɗarin.

Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kuma an samu gibi a cikin labarin mutumin, ’yan sanda sun gano cewa wani mutumin Florida ya ziyarci mutumin da ake zargi da cire kafafu da gatari kuma an yi zargin ya sare kafafunsa, kan kuɗi ne.

Daga baya an bayyana cewa mutumin dai ya shirya wani shiri na yin damfarar inshora, kuma da yake ba ya da wani amfani ga kafafunsa kuma, sai ya yanke shawarar yanke su a wani haɗarin da ya rutsa da shi.

Amma tunda har yanzu mutumin bai shigar da kuka a kamfanin inshorar ba, babu dalilin da zai sa a tuhume shi da laifi.

Thompson ya ce, “Tsarin da ba a shirya ba aka yi ne, ban taba ganin wani abu mai kama da haka ba.”

Kodayake ba za a iya tuhumar mutumin ba da laifin zamba a hukumance ba, ofishin Sherif ya fusata da bata masa lokaci har ya yi la’akari da tuhumar shigar da rahoton ’yan sanda da rahoton EMS a matsayin na karya.

Matsalar ita ce, raunin da mutumin ya yi, ya yi muni sosai ta yadda zaman gidan yari ba zai yiwu ba.

Don haka sai shugaban ya yanke shawarar bari ya warke a asibiti tukunna.

Dangane da kafafun mutumin da suka bace, rahotanni sun ce wani dan uwansa ya same su a cikin wata guga ta tayoyi a boye ya mika su ga masu bincike.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta