Ya sa dansa yin bara a tashar jirgin kasa don ladabtarwa
Wani mahaifi dan kasar Chana ya sa dansa yin bara a tashar jirgin kasa ta Shanghai a matsayin ladabtarwa saboda rashin yin gwajin karatun da aka umarce shi a makaranta idan ya koma gida. A safiyar Alhamis din makon jiya ne, ’yan sandan Shanghai suka amsa kiran wayar gaggawa cewa wani dalibi na duke yana […]
Wani mahaifi dan kasar Chana ya sa dansa yin bara a tashar jirgin kasa ta Shanghai a matsayin ladabtarwa saboda rashin yin gwajin karatun da aka umarce shi a makaranta idan ya koma gida.
A safiyar Alhamis din makon jiya ne, ’yan sandan Shanghai suka amsa kiran wayar gaggawa cewa wani dalibi na duke yana barar neman abinci a tashar jirgin kasar garin. Lokacin da ’yan sandan suka isa sun gano yaron mai shekara 10 yana dauke da wata robar bara yana tambayar mutane abinci. Da aka tambaye shi yadda aka yi ya zo wajen, sai ya ce mahaifinsa ne ya bar shi a tashar jirgin kasar kimanin minti 45, ya dora masa robar bara a ka, sannan ya umarce shi ya roki matafiya a matsayin ladabtarwa saboda rashin bin umarnin malaman makarantarsa.
Yaron ya bayyana wa ’yan sandan cewa, an kai kararsa wajen malaman makarantar kan bai kammala abin da aka sa shi ya yi ba. Don haka mahaifinsa ya umarce shi ya tsugunna ya yi bara a wajen jama’a.
’Yan sandan sun dauki yaron zuwa ofishinsu daga nan suka ba shi biskit da shayi, sannan suka nemi mahaifiyarsa ta zo ta dauke shi, bayan kamar awa daya. Ta bayyana wa ’yan sandan cewa, mijinta ya fusata ne da dan nasu saboda bai bi umarni makarantarsa ba, don haka ya umarce shi ya yi bara a tashar jirgin kasa da nufin cewa idan bai yi karatu ba a haka zai kare yana bara. Amma duk da haka mahaifiyar yaron ba ta amince da wannan hukunci ba.
Rahoton bai bayyana ko hukumar ta hukunta mahaifin yaron ba saboda abin da ya yi wa yaron, amma a cewar kafar sadarwa ta Kankannews.com, jami’an tsaron sun gargadi mahaifiyar yaron game da irin wannan hukuncin da aka yi wa yaron cewa zai iya rage kima da martabar zuriyarsu.
Irin wannan horarwar sabon abu ne a kasar China, duk da yake ana sukar hukuncin da mahaifin ya yi wa dansa a shafukan sadarwa na zamani, kadan ne suka nuna goyon bayansu game da irin wannan hukunci.
“Da wata irin manufa mahaifin ya aikata wannan hukuncin? Aikata wannan hukuncin zai iya haifar da wani abu ga dansa a kurarren lokaci. Allah Ya taimaka ’yan sanda sun shiga cikin lamarin,” Kamar yadda wani ya yi martani a kafar sadarwar.
Wani kuma ya yi bayanin cewa, misalin a ce mahaifin yaron yana cikin talauci ne da abin da zai aikata sai ya fi haka. Yaro ya yi bara a tashar jirgin kasa babban hadari ne ga rayuwar yaron.