Ya ‘sace’ wayar dan sanda a caji ofis lokacin da ya je neman beli
Ya sace wayar ta N120,000 ne lokacin da ya je belin abokinsa
Mutane sun cika da mamaki lokacin da aka gurfanar da wani mutum mai shekara 45, a gaban kotu bisa zarginsa da satar wayar dan sanda da darajarta ta kai Naira 120,000.
An dai gurfanar da shi ne a gaban kotun Majistare da ke Ogba a jihar Legas ranar Juma’a.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Ciranin Katsina Ke Safarar Makamai Daga Legas
- Cutar ‘Haukan kare’ na kama ’yan Najeriya 55,000 a duk shekara – USAID
’Yan sanda sun ce lamarin ya faru ne lokacin da wanda ake zargin ya je caji ofis dinsu da ke Bolade, domin yin belin abokinsa da aka tsare.
Dan sanda mai gabatar da kara, Rachael Williams, ya ce wanda ake zargin ya shiga ofishin ne lokacin da wayar ke ajiye a kan tebur.
Kodayake ya musanta zargin satar wayar, amma ’yan sanda duk da haka sun gurfanar da shi kan zarge-zargen sata da shiga ofishin ba bisa ka’ida ba.
A cewar Rachael, gano satar wayar ya jefa ’yan sandan da ke bakin aiki cikin rudani, inda nan take Baturen ’Yan Sandan ofishin ya ba da umarnin gudanar da bincike.
Alkalin kotun, Mai Shari’a O.O. Akingbesote, ya bayar da wanda ake zargin beli a kan Naira 100,000 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa.
Daga nan ne alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar tare da ba da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali na Kirikiri.